--
Direba ya gane wanda ya taɓa garkuwa da shi cikin fasinjojin da suka shiga motarsa a Sokoto

Direba ya gane wanda ya taɓa garkuwa da shi cikin fasinjojin da suka shiga motarsa a Sokoto


Direba ya gane wanda ya taba garkuwa da shi daga cikin fasinjojin sa a tashar Kwannawa da ke jihar Sokoto - Direban wanda aka yi garkuwa da shi watanni biyu da suka gabata a Kankara da ke jihar Katsina ya yi saurin gane mutumin kuma ya sanarwa da shugabbanin tashar 


Yan sanda sun kama wanda ake zargin kuma tuni aka maida al'amarin zuwa hedikwatar yan sanda ta Sokoto don fadada bincike Wata dambarwa ta faru a tashar mota ta Kwannawa da ke Karamar Hukumar Dange-Shuni a jihar Sokoto 


bayan da wani direba ya shaida wanda ya yi garkuwa da shi a cikin fasinjojinsa. Direban wanda ba'a bayyana sunan shi ba, an yi garkuwa da shi a Kankara da ke jihar Katsina watanni biyu da suka gabata. 


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa direban ya shafe kimanin sati uku a tsare bayan biyan kudin fansar da ba'a bayyana adadin su ba. 


Wanda ake zargin ya gamu da cikas, lokacin da ya shiga mota zuwa Kano, ba tare da sanin ita ce motar da suka tare suka yi garkuwa da direba ba. 


"Direban ya yi saurin gane shi saboda abin bai dade da faruwa ba. "Bayan gane shi, ya yi gaggawar sanar da Shugabannin kungiya su kuma suka sanar da yan sanda mafi kusa," wani dan kungiyar direbobi NURTW ya shaidawa manema labarai. 


Shugabannin Kungiyar sun chanja direban motar da wani bayan motar ta cika da fasinja kuma ya nufi garin Shuni. An ruwaito cewa a nan yan sanda suka kama wanda ake zargin zuwa ofishin su. 


Da ake tuhumar sa, ya bayyana cewa shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne kuma ana kiran sa 'Hadari' kuma aka hada shi da direban don amsa tambaya. "Yan sanda sun yi mamakin yadda yadda direba ya fadi sunan duk da baya nan lokacin da ake tuhumar," 


a cewar majiyar mu. An mayar da wanda ake zargin zuwa hedikwatar yan sanda ta jihar Sokoto don fadada bincike. Mai magana da yawun rundunar, DSP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce bincike su ke har yanzu. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Direba ya gane wanda ya taɓa garkuwa da shi cikin fasinjojin da suka shiga motarsa a Sokoto "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?