--
Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 (hotuna)

Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 (hotuna)

 


Kasar Najeriya ta cika shekaru 60 da samun yancin kai a yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020 


Manyan jaruman Kannywood basu bari an barsu a baya ba wajen raya wannan rana - Jaruman masa'antar da dama sun wallafa sakon taya murna a shafukansu 



dauke da hotuna sanye da kaya kalar tutar Najeriya na kore da fari A yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020 ne yan Najeriya ke murnar cikar kasar shekaru 60 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka. 


Dubban yan Najeriya na cike da murnar wannan rana duk da cewa akwai kalubale daban-daban da kasar ke fuskanta. 


Saboda haka ne yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ma suka fito suna nuna nasu farin cikin. Jaruman masa’antar da dama sun wallafa hotunansu da rubuce-rubuce domin raya wannan rana a shafukan soshiyal midiya. 


An gano jaruman sanye da tufafi launin tutar Najeriya, wato kore da fari. Ga wasu hotuna da wasu fitattun jaruman na Kannywood suka wallafa a shafukansu na sada zumunta. 


Fitaccen jarumi Ali Nuhu wanda aka fi kira da Sarkin Kannywood, ya wallafa wannan hoton tare da cewa: ''Yancin kai da yanci na gaskiya kan samu ne kawai ta hanyar yin abin da ya dace. 


A matsayinmu na yan Najeriya, kasarmu da muke kauna, muna bukatar yin abin da ya dace don ganin sauyin da ko yaushe muke magana a kansa ya samu. Kasarmu ta cika shekara 60, dole mu yi fafutuka a tare don tabbatar da martabarta.'' 




 

A nata sakon taya murnar samun yancin kai, Fati Washa ta wallafa: ''Ku zo mu daga hannu don murnar wannan ranar tare da yin bikinta. Ku zo mu tashi tsaye don nuna girmamawarmu ga jagororin da suka mutu a fafutukar nemo mana yanci. 


Ku zo mu rera takenkasarmu dauke da tutoci a hannayenmu don bikin wannan rana mai muhimmanci.'' 



A bangarensa Sani Danja ya ce: ''Yaranmu na yau, shugabannin gagarumar kasarmu Najeriya. Barka da zagayowar ranar samun yancin kai Najeriya.'' 



Mansura Isah kuma ta wallafa: ”Babu wani waje da ya kai gida. Barka da zagayowar ranar samun yancin kan Najeriya.'' 




 Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 (hotuna) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?