--
Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu

Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu




Amzat Ibrahim mawaki ne kuma mazaunin garin Ibadan da ke jihar Oyo - Ya tabbatar wa da kotu cewa turmi da tabarya ya kama matarsa da amininsa - Ya sanar da yadda matarsa ta kwashe yaransa na tsawon wata uku amma sai a gidan abokinsa ya ganta Wani mawaki mai suna Amzat Ibrahim, a ranar Alhamis ya sanar da wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun a Ibadan cewa matarsa fasika ce. 


Ya sanar da yadda matarsa mai suna Zainab take lalata da babban amininsa. Amzat ya bayyana wannan zargin ne bayan Zainab ta sanar da kotun cewa yana farautar rayuwarta domin haka take so a raba aurensu. "Mai shari'a, a gaskiya ni da Zainab muna fada ne saboda halin bin mazanta. Zainab da babban abokina suna fasikanci. 


“Ta yi batan dabo na tswon watanni uku inda ta bar gidana. Ta kwashe yarana amma daga bisani sai na gano tana gidan abokina ne kuma amini. "Dumu-dumu na kama su suna faskancin," Amzat yace. Kamar yadda mai karar wacce ta mallaki mashaya ta fara sanar da kotun, ta ce mijinta yana barazanar raba ta da rayuwarta. 


Ta zargesa da tozartata tare da zaginta a cikin jama'a da kuma cikin gari. "A koda yaushe yana bibiyar duk inda naje," matar ta sanar. Alkalin kotun, Chief Henry Agbaje, ya shawarci ma'auratan da su tabbatar da ikirarinsu nan gaba a gaban kotun. Ya ce kowannensu ya bayyana da 'yan uwansa biyu a zama na gaba. Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?