--
Sojoji sun sheke Abubakar Haruna, dillalin makaman 'yan bindigar Katsina

Sojoji sun sheke Abubakar Haruna, dillalin makaman 'yan bindigar Katsina


Rundunar soji ta fitar da sanarwar samun nasarar kashe Abubakar Haruna, shahararren mai safarar makamai - Manjo Janar John Enenche, darektan watsa labaran atisayen rundunare soji, ya ce an kashe Haruna ne a yankin karamar Dutsinma, jihar Katsina 


Wasu jihohin arewa da suka hada da Katsina, Sokoto, da Zamfara na fama da yawaitar kaiwa jama'a hare-hare da 'yan bindiga ke yi Sojojin rundunar Atisayen Haɗarin Daji sun sheƙe shahararren mai safarar makamai wanda aka sani da Abubakar Haruna. 


Sojojin sun kuma kashe gawurtattun ƴan fashi har guda huɗu a atisaye daban-daban da suka gudanar a tsakanin 15 zuwa 21 ga watan Oktoba. Darektan sashen watsa labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja lokacin da yake gabatar da bayanan mako a kan aiyukan atisayen rundunar soji. 


Mr Enenche ya bayyana cewa an samu carbi 600 na alburushi mai tsawon 7.62mm daga wurin dillalin makamai Haruna. An kashe wanda ake zargin a kan hanyar zuwa garin Tsakiya da ke yankin ƙaramar hukumar Dutsinma a Jihar Katsina. 


Enenche ya kara da cewa; ''a ranar 15 ga watan Oktoba, sojoji sun tilastawa wasu ƴan fashi da makami guduwa bayan sun kai farmaki ƙauyen Rawayu a ƙaramar Kurfi ta jihar Katsina inda suka kashe huɗu daga cikinsu wasu kuma suka tsere da muggan raunaka sakamakon harbin bindiga.''


A cewar Enenche; ''a ranar Juma'a, 16 ga watan Oktoba, sojoji sun kama mai haɗin guiwa da ƴan fashi a mahaɗar Shema da ke yankin ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina. 


"Kazalika, sojojin sun yi nasarar kama mutum biyu da ake zargin ƴan fashi ne a kasuwar Magami da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.'' 


Janar Enenche ya ce waɗanda ake zargin sun kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da sace mutane 13 a ranar Litinan 21 ga watan Satumba. ''Sojoji na cigaba da kubutar da al-umma da samun nasara a yaƙi da fashi da makami, satar shanu, da sauran manyan laifuka a yankin arewa maso kudu. 


"Waɗannan nasarori da aka samu cikin ƙanƙanin lokaci hujja ce da ke nuni da cewa sojoji a shirye suke kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu," a cewarsa. Sannan ya kara da cewa; ''dakarun soji sun maida hankali don ganin sun kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Arewa maso yamma da ma sauran sassan Najeriya.'' 


Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Sojoji sun sheke Abubakar Haruna, dillalin makaman 'yan bindigar Katsina "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?