--
Na yi nadamar jagorantar kafa rundunar SARS - Tsohon dan sanda Kwajaffa

Na yi nadamar jagorantar kafa rundunar SARS - Tsohon dan sanda Kwajaffa


Malam Fulani Kwajafa ya nuna alhininsa akanrundunar 'yan sanda ta SARS din da aka rusa - Tsohon dan sandan yace an kirkira rundunar ne don yaki da fashi da makami a fadin kasar nan 


Jaridar Legit.ng ta gane cewa yana daya daga cikin 'yan sandan da suka kirkiri SARS a mulkin Buhari na soji a 1984 Fulani Kwajafa, tsohon dan sanda ne wanda ya jagoranci kirkirar SARS, ya nuna danasaninsa na kirkirar rundunar a hirarsa da BBC Hausa a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba. 


Ana tsaka da zanga-zangar rushe rundunar, Kwajafa yace an kirkire su ne don yaki da fashi da makamai a fadin Najeriya. Kwajafa ya sanar da yadda aka kirkiri SARS a shekarar 1984, lokacin Etim Inyang ne sifeto janar na 'yan sanda lokacin Buhari na Shugaban kasa na mulkin soji. 


"Amma sai dai daga labaran kungiyar da nake ji, sun canja salon aikin nasu, duk sai naji takaici da danasanin kirkirar kungiyar," yace. Tun daga ranar Alhamis din makon da ya gabata ne matasa a yankin kudancin kasar nan da babban birnin tarayya suke zanga-zanga. 


Suna yin hakan ne domin neman a rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makamai a fadin kasar nan. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Na yi nadamar jagorantar kafa rundunar SARS - Tsohon dan sanda Kwajaffa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?