--
Matashi mai digiri ya adana kwalinsa, ya fada harkar noma kuma yana samun nasarori

Matashi mai digiri ya adana kwalinsa, ya fada harkar noma kuma yana samun nasarori

 Sau da yawa, mutum na samun nasara ta bangaren da bai yi zato ba, duk da kushe da mutane daban-daban za su yi 

Wani matashi dan asalin jihar Imo, mai suna Eke William yace tarkonsa ya kama kurciya - Saurayin yayi digiri a jami’ar jihar Imo a fannin kasuwanci, amma ya kama harkar noma inda arzikinsa ya tumbatsa Wani lokacin, jama’a na samun nasara a wasu harkokin arziki wadanda basu da alaka da karatun da suka yi a makaranta. 


Hakika noma tushen arziki ne a wurin Eke William, wani dan Najeriya da ya kammala digirinsa akan harkar kasuwanci a jami’ar jihar Imo a shekarar 2016. 


Dan asalin kauyen Umuohiago da Ngor Okpala dake jihar Imo ya wallafa irin arzikin da ya samu a harkar noman gurji a kafar sada zumuntar zamani. 

Ya bayyana yadda abokai da ‘yan uwansa suka yi ta sukar noma, suna ganinta ya za’ayi mai digiri ya koma harkar noma, kamar ya ci baya kenan. Amma yanzu sai gashi ya samu nasara da kuma habakar arziki. 


Matashi mai digiri ya adana kwalinsa, ya fada harkar noma kuma yana samun nasarori Source: Original A yadda Eke ya yiwa wakilin Legit.ng, Victor Duru, bayani a wata zantawa da suka yi. Yace da farko wani abokinsa ya kashe masa jiki lokacin da yace zai yi noman gurji. Matashin manomin ya ci nasara duk da yadda abokansa suka yi ta nuna masa cewa ba zai iya ba. Ya sanar da irin ribar da ya samu mai yawa. 


Mutane da dama sun yi ta mamaki yadda za’ayi dan boko irin Eke ya tsaya a harkar noma, amma hakan bai karya masa jiki ba. A wani labari na daban, Belinda Effa, jarumar Nollywood ta wallafa hoton wata mata wanda ya ba kowa dariya. 


A Bidiyon, wata mata ce a cikin jirgin sama, wadda ta bukaci a dakata da tashin jirgin don ta fita, saboda bata so a ajiye mata jakarta mai tsada a kasa ko kuma a ajiye jakar a ma'ajiyar cikin jirgin.


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Matashi mai digiri ya adana kwalinsa, ya fada harkar noma kuma yana samun nasarori"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?