--
 (Kalli Bidiyo):Yanda Matasa suka ƙona gidan sanata a Nigeria Suka kwashe kayayyaki masu muhimmanci

(Kalli Bidiyo):Yanda Matasa suka ƙona gidan sanata a Nigeria Suka kwashe kayayyaki masu muhimmanci


Ana ci gaba da kai hare hare kan gidajen manyan 'yan siyasa duk da dokar ta baci da aka saka a wasu jihohi - Wasu matasa sun yi kutse cikin gidan Sanata Gershom Bassey da ke birnin Calabar a jihar Cross Rivers 


Matasan da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun yi wa jami'an tsaro karfa-karfa sannan suka samu ikon shiga gidan Wasu da ake zargin 'yan daba sun ne sun kai hari gidan iyayen Sanata Gershom Bassey da ke wakiltan Calabar South a ranar Asabar 24 ga watan Oktoba. 


'Yan daban sun sace kayayyaki daga gidan da ke Calabar, babban birnin jihar kana daga bisani suka cinna wa gidan wuta. 


Bidiyon yadda abin ya faru dake yawo a yanar gizo, ya nuna wasu matasa sun dauki katifa, talabijin, kujeru da kuma tukunyar gas daga gidan. 

News Wire NGR ta ruwaito cewa maharan sunyi wa jami'an tsaron dake tsaron gidan karfa- karfa kafin su sami damar shiga ginin. 

Wasu yan ta'adda kuma, sun shiga gidan tsohon shugaban majalisar dattawa, Victor Ndoma Egba a Calabar suka kuma yi awon gaba da wasu kayayyakin amfanin gida, suka kuma lalata motoci. 



Gidajen manyan yan siyasa irin su Ndoma Egba da Liyel Imoke suna ci gaba da fuskantar hare hare duk da dokar ta baci da aka saka a jihar. Ndoma Egba ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Nuwambar 2015. 


Shine mataimakin shugaban majalisa ta 6 (2007- 2011) kuma shugaban majalisar (2011 - 2015). An nada shi a matsayin shugaban hukumar ci gaban Niger Delta (NDDC) a Yuli 2016. 




 Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to " (Kalli Bidiyo):Yanda Matasa suka ƙona gidan sanata a Nigeria Suka kwashe kayayyaki masu muhimmanci"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?