--
Ganduje ya dauki matakin dakatar da zanga-zanga a Kano bayan an kone motoci

Ganduje ya dauki matakin dakatar da zanga-zanga a Kano bayan an kone motoci


An samu barkewar wata kwarya-kwaryar zanga-zanga a Kano ranar Talata - Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa zanga-zangar ba ta da alaka da zanga-zangar ENDSARS da ake yi a wasu jihohin kudancin Najeriya


 Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ta shawo kan lamarin, yanzu komai ya koma daidai Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta sanar da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon zanga-zangar da ta barke ranar Talata a yankin unguwar Sabon Gari da ke birnin Kano. 


Sai dai, rundunar ta sanar da cewa ma su zanga-zanga sun lalata motoci goma sha biyar. Rundunar ta kafe a kan cewa zanga-zangar da ta barke a Kano ba ta da wata nasaba da zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS. 


Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Habu Sani, ya sanar da cewa an kama wani mutum da ake zargi da harba bindiga yayin zanga-zangar ta ranar Talata. 


CP Sani ya bayyana cewa an lalata motoci 15, an kone guda bakwai tare da kwankwatse wasu guda takwas. Kazalika, ya ce ma su zanga-zangar sun tafka barna a shagunan 'yan kasuwa. 


A daren ranar Talata ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kira wani muhimmin taro da shugabannin kabilu daban-daban da ke Kano domin kare yaduwar rikicin da ya barke sakamakon zanga-zangar ENDSARS a sassan Najeriya. 


A cikin jawabin da kakakinsa, Abba Anwar, ya fitar ranar Laraba, Ganduje ya bawa dukkan mazauna Kano tabbacin samun tsaro. 


A cewar sanarwar da Anwar ya fitar, ''gwamnatin jihar Kano ta gana da ma su ruwa da tsaki a kan lamarin, kuma muna aiki kafada-kafada tare da hukumomin tsaro. "Kyakyawar alakar gwamnatinmu da hukumomin tsaro ta taimaka wajen samun zaman lafiya a jihar Kano.


"Mun zauna tare da tattaunawa da shugabannin kabilu daban-daban a daren da ya gabata kuma sun bamu tabbacin cewa za su fadakar da mutanensu tare da kwantar mu su da hankali, wanda hakan zai kawo dorewar zaman lafiya." 


Ganduje ya bayyana cewa, "an samu barkewar zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya da suka hada da Kano, amma yanzu mun shawo kan lamarin, babu wani sauran tarnaki'' 


Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Ganduje ya dauki matakin dakatar da zanga-zanga a Kano bayan an kone motoci "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?