--
Gabas Ta Tsakiya: Takunkumin hana Iran sayen makamai ya kare

Gabas Ta Tsakiya: Takunkumin hana Iran sayen makamai ya kare

 


Majalisar Ɗinkin Duniya za ta cire wa Iran takunkumin hana ta sayen makamai daga yau Lahadi.


Hakan na cikin yarjejeniyar da a ka kulla da gwamnatin da ke Tehran a shekarar 2015, kan batun mallakar makamin nukiliya.


Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce daga yanzu ƙasarsa na da damar mallakar makamai ta kowa ce hanya ta ke so ba tare da wasu ka'idoji ba na kasa da kasa.


To amma Mista Rouhani ya kara da cewa hakan ba yana nufin za su yi ta sayen makaman ba ba ji ba gani ba ne.


Shugaban ya ce tun bayan da su ka shafe shekaru da takunkumin hana mallakar makamai ma'aikatar tsaron kasar ta fara tunanin kera na ta na kanta.


Amurka ta yi ta kokarin ganin cewa an tsawaita matakin hana Iran mallakar makaman, to amma kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi watsi da wannan bukata.


Source: Bbchausa

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Gabas Ta Tsakiya: Takunkumin hana Iran sayen makamai ya kare"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?