--
EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

 


Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da tsinke wa wani dan sanda kai kuma aka banka masa wuta - Hakan ta faru sakamakon harin da wasu 'yan daba masu zanga-zanga suka kai ofishinsu da ke Nnewi 


Kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatar da mutuwar wasu mutum uku cikin biyar a asibitin garin A ranar Alhamis ne wasu mutane da ake zargin 'yan daba suka tsinke kan dan sanda tare da kone shi kurmus yayin zanga-zangar EndSARS a Nnewi da ke jihar Anambra. 



Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu 'yan sandan uku sun samu miyagun raunika. Ya ce an gaggauta mikasu asibiti domin samun taimakon likitoci na gaggawa, 


The Nation ta ruwaito. Ya ce an an kai wa wasu mutum biyar hari a Onitsha kuma an kai su asibiti inda ake kula da su amma uku daga cikinsu sun rasu. 


Ya kara da bayyana cewa, masu zanga-zangar sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke Nnewi, sun banka masa wuta tare da kone motocin sintiri. Kamar yadda yace, "A ranar 21 ga watan Oktoba wurin karfe 11:30 na dare, 'yan daba masu tarin yawa da suka fake da zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke Nnewi, 


sun banka masa wuta tare da kone ababen hawa na sintiri. Sun kwashe makamai masu yawa. "Hakazalika, a ranar 22 ga watan Oktoban 2020 tsakanin karfe 3:30 na safe zuwa 5 na yamma, sun kashe dan sanda daya sannan suka banka masa wuta. Wasu ukun sun samu miyagun raunika amma an garzaya da su asibiti." 


Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?