--
El-Zakzaky bai Mutuba yana nan da ransa - Inji ''yan shi'a

El-Zakzaky bai Mutuba yana nan da ransa - Inji ''yan shi'a

 


Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da Shi'a ta karyata labarin cewa shugaban ta Ibrahim Zakzaky ya mutu 


Wani mamba a kungiyar mai suna Abdullahi Usman ya tabbatar da cewa shugaban su yana nan da ransa - Jita-jitar rasuwar Zakzaky ya bazu a garin Kaduna inda ya jefa tsoro zukatan mutane har wasu sun takaita zirga-zirga 


Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Shiekh Ibrahim El-Zakzaky yana nan da ransa kamar yadda wani dan kungiyar mai suna Abdullahi Usman ya tabbatar. 


Daily Trust ta ruwaito cewa akwai jita-jita da ke yawo na cewa shugaban kungiyar da IMN da ake yi wa lakabi da Shi'a ya mutu. Amma Usman yayin hira da majiyar Legit.ng ta yi da shi ta wayar tarho ya tabbatar da cewa Zakzaky yana nan bai mutu ba. 


"Ban san daga inda mutane suka jiyo wannan jita-jitar ba, amma ina tabbatar maka cewa shugaban mu yana nan da ransa. Ba zai haifar wa gwamnati da mai ido ba idan shugaban mu ya mutu a hannun ta," 


ya kara da cewa. Daily Trust ta ruwaito cewa labarin rasuwar Zakzaky ya jefa mutane cikin halin dar-dar a Kaduna inda wasu suka takaita zirga zirga don tsoron hari. 


Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "El-Zakzaky bai Mutuba yana nan da ransa - Inji ''yan shi'a"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?