--
Tirkashi: Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas

Tirkashi: Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas


Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa dalibai 181 na wata makarantar kwana dake Lekki sun kamu da cutar COVID-19 - Farfesa Akin Abayomi, kwamishanan lafiyan jihar ya bayyana hakan da yammacin Juma'a 


Abayomi yace wata dalibar ajin SS1 ta fara rashin lafiya ranan 3 ga Oktoba kuma aka kora ta gida bayan karamin jinya a makarantar Wani rahoton The Nation ya nuna cewa dalibai da malaman wata makaranta mai zaman kanta dake unguwar Lekki, a jihar Legas sun kamu da mugun cutar Korona. 


Legit.ng ta tattaro cewa kwamishanan lafiyan Legas, Akin Abayomi, ya ce an gano sun kamu da cutar ne bayan binciken da aka gudanar a makarantar. Kwamishanan yayinda yake bayanin binciken, ya ce wata daliba mai shekara 14, yar ajin SS1 ta fara lafiya ranar 3 ga Oktoba kuma aka tura ta gida bayan karamin jinyar da tayi a makarantan. 


Ya kara da cewa kwana uku bayan hakan wani dalibi ya kamu da cutar bayan gwajin da akayi masa ranar 6 ga Oktoba. Abayomi ya tabbatarwa yan jihar Legas cewa gwamnatin na daukan matakan da ya kamata domin shawo kan lamarin. 


Ya bayyana cewa an sanar da dukkan iyaye kuma an shawarcesu kan abinda ake ciki a ranar 13 ga Oktoba. An tattauna da iyayen ne a taron Zoom na yanar gizo. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765



0 Response to "Tirkashi: Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?