--
Da duminsa: NECO ta dakatar da jarabawa, ta umarci ma'aikata su koma gida

Da duminsa: NECO ta dakatar da jarabawa, ta umarci ma'aikata su koma gida


Bayan tabarbarewar harkokin tsaro a jihohin Najeriya, hukumar shirya jarabawar NECO ta dakatar da cigaba da rubuta jarabawoyin da suka rage 


Bayan hukumar ta gano cewa wasu daga cikin daliban basu samu damar rubuta jarabawoyin da aka yi ranar Talata da Laraba ba saboda zanga-zanga da kulle


Hukumar ta ce rayuwar dalibai da malamai masu kula da jarabawar na cikin hatsari, don haka ta dakatar da jarabawar har sai bayan al'amura sun lafa Bayan tabarbarewar harkokin tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS, NECO sun dakatar da jarabawarsu da daliban ajin karshe na sakandare suke yi. 


Jaridar THISDAY ta gano yadda hukumar shirya jarabawar ta umarci masu jarabawa da masu kula da su a ofisoshi daban-daban da su dakatar har sai sun bada wata sanarwa nan gaba,


Umarnin dakatar da cigaba da rubuta jarabawar ya biyo bayan kullen awanni 24 da gwamnatin jihohi kamar Legas, Ogun, Edo da Imo suka sa sakamakon canja akalar da masu zanga-zangar dakatar da SARS suka yi. 


Hukumar shirya jarabawar ta yi jarabawoyi biyu, daya ranar Talata daya Laraba, babu wasu dalibai sakamakon kullen da kuma zanga-zangar. 


Don haka shugaban hukumar shirya jarabawar NECO ta bada umarnin dakatar da jarabawar sai lokacin da al'amura suka daidaita. Don haka ta dakatar da jarabawoyin ranar Alhamis, 22, Juma'a 23 da Asabar 24 ga watan Oktoba zuwa 17 zuwa 19 ga watan Nuwamba wanda za'ayi a na'ura mai kwakwalwa. 


A wani labari na daban, bayan yunkurin kai wa gidan talabijin din Channels da sa'o'i biyu, sun cigaba da aikinsu. A ranar Laraba da safe ne aka ga gidan talabijin din ya dauke, bayan rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'adda na hanyar kawo wa gidan talabijin din TVC farmaki.


 'Yan jarida da ma'aikatan gidan talabijin din sun tsere saboda tsoron a kawo musu hari, The Cable ta wallafa. 



Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da duminsa: NECO ta dakatar da jarabawa, ta umarci ma'aikata su koma gida "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?