--
Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda

Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda




Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas ya sanar da cewa an harba jami'ansu uku a ranar Litinin - Muyiwa Adejobi ya tabbatar da cewa masu zanga-zanga suna kai musu hari har ofishinsu a jihar Legas 


Masu zanga-zangar dai sun hada da matasa masu bukatar a kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yi wa jama'a Rundunar 'yan sandan jihar legas ta ce masu zanga-zanga sun harba jami'anta uku a ranar Litinin. 


Jaridar The Cable ta wallafa yadda masu zanga-zanga suka rufe titunan Lekki, Surulere da Ikeja a jihar Legas inda suke bukatar a gyara tsarin ayyukan 'yan sanda. 


Bayan zanga-zangar matasa a dukkan fadin kasar nan, Mohammed Adamu, Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya ya sanar da rushe rundunar 'yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami. 


Amma kuma har yanzu matasa masu zanga-zangar sun ki barin titunan. A yau ne jaridar The Nation ta bayyana cewa matasa sun kai wa ofishin 'yan sanda a jihar Legas hari. A kalla masu zanga-zanga biyu 'yan sanda suka harba a yankin Surulere da ke jihar legas a ranar Litinin. 


An gano cewa hakan ya faru ne bayan da 'yan sanda suka bude wa masu zanga-zangar ruwan wuta. A wata tataunawar waya da aka yi da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya ce an harba 'yan sanda uku a ranar Litinin. 


Adejobi ya ce bashi da labarin mutuwar ko daya daga cikin masu zanga-zangar, amma ya kara da cewa sun kai hari ofishin 'yan sandan. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?