--
Da dumi-dumi: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya

Da dumi-dumi: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya


Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya 

Minista Adamu Adamu ya sanar da hakan madadin gwamnati Yanzu an baiwa dukkan makarantu masu zaman kansu damar budewa ranar da suka ga dama Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, 


ya sanar da umurnin bude dukkan makarantun Firamare, Sakandare, da jami'o'i a Najeriya. Adamu ya sanar da hakan ranar Juma'a a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Premium Times ta ruwaito. 


Ya bada shawaran cewa dukkan makarantun su bi ka'idojin da aka gindaya na bude makarantu da kwamitin yaki da cutar Korona PTF ta sanar. 


Tuni dai Ministan Ilimin ya sanar da ranar bude makarantun gwamnatin tarayya a fadin kasar ranar 12 ga watan Octoba, 2020. "Amma jihohi da makarantu masu zaman kansu zasu iya budewa duk ranar da suka ga dama." Yace 


Adamu yace anyi hakane domin aba daliban da suka dade zaune a gida damar kammala zangon karantunsu wanda zai kare karshen disamba.


Ministan ya bada shawara akan abi ka'idojin kare kai daga cutar Covid-19 a makarantun domin takaita yaduwar ta tsakanin dalibai.


"Har ila yau, Makarantun da basu kammala zangon karantunsu na biyu ba suyi kokari su kammala sannan su shiga zangon karatu na uku wanda ake sa ran zai kare a watan disambar 2020, "A cewar shi. 


Jihohi da dama irinsu Lagos, Oyo, Kano da Enugu tuni sun sanar da ranakun bude makarantunsu. A bangare guda, A ranar Laraba, 30 ga watan Satumba, 


kungiyar ASUU ta malaman Jami’an Najeriya ta yi magana game da yajin-aikin da ta dauki tsawon lokaci ta na yi. ASUU ta bayyana cewa ba ta da shirin janye yajin-aiki har sai gwamnati ta biya ta bashin albashin watanni uku zuwa bakwai da malaman jami’a su ke bi.


 Bayan haka, ASUU ta ce dole a amince da manhajar UTAS da su ka kawo domin a rika biyan albashin malaman jami’o’i, idan ana so a bude makarantu. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Da dumi-dumi: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?