--
Bidiyon wani mai bayar da hannu a titi da masu zanga-zanga suka karrama saboda kwazonsa

Bidiyon wani mai bayar da hannu a titi da masu zanga-zanga suka karrama saboda kwazonsa


A kwanan nan ne aka karrama wani dan sanda mai bayar da hannu a titi a yayinda yake bakin aiki - A cewar rahotanni, wasu masu zanga-zanga a Calabar sun taru domin karrama shi saboda kwazonsa 


A wani bidiyo da aka wallafa, an gano inda masu zanga-zangar suka daga mutumin sama sannan suka ta yi masa liki da kudi Wasu masu zanga-zangar a kawo karshen SARS a garin Calabar, sun karrama wani dan sanda mai bayar da hannu a titi, sun nuna masa so da kauna tare da tallafa masa. 



A wani bidiyo da shafin @mediagist ta wallafa a Instagram, an nuno yadda matasan suka karrama mutumin tare da taya shi murna a yayinda yake bakin aikinsa. A bisa ga wallafar, an bayyana mutumin mai suna Igri Nna Nkanu, a matsayin jajirtacce kuma mai kwazo a kan aikinsa.


Taron wanda ya gudana a ranar Juma’a, 16 ga watan Oktoba, ya nuno yadda mutane suka taru a kanshi, sannan suka daga shi sama a kan kokarin da yake yi kan aikinsa. A cikin bidiyon, an gano wasu masu zanga-zanga suna masa liki da kudi. Wani mai amfani da Twitter @JC_Jokes ya wallafa bidiyon inda ya rubuta: 


“Masu zanga-zanga sun karrama mai bayar da hannu a titi mafi kwazo a Calabar. A koda yaushe za ku ganshi yana aikinsa da murmushi a fuskarsa a hanyar Mary Slessor. Har tara masa kudi suka yi. Yan Najeriya sun kasance mutane masu karamci duk da halin da ake ciki!”  




 Source:Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Bidiyon wani mai bayar da hannu a titi da masu zanga-zanga suka karrama saboda kwazonsa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?