--
Barron Trum: Coronavirus ta kama ɗan autan Shugaba Trump

Barron Trum: Coronavirus ta kama ɗan autan Shugaba Trump


Dan shugaban Amurka Donald Trump wato Barron mai shekaru 14, ya kamu da cutar korona, amma a yanzu gwajin da aka yi masa ya nuna cewa baya dauke da cutar.


Uwargidan shugaban kasar Melania Trump ta bayyana cewa "tsoronta ya zama gaskiya" lokacin da aka tabbatar Barron ya kamu da cutar.


Sai dai ta ce kasancewar sa saurayi ne mai ƙarfi a jika, bai nuna wasu alamun cutar ba.


Shugaba Trump da mai dakin ta sa duk sun kamu da cutar a baya bayan nan, tare da wasu sauran ma'aikatan fadar White House, sai da tuni suka murmure.


Kafin ya tafi taron yakin neman zabensa Iowa a ranar Laraba, Mista Trump, ya fada wa manema labarai a Fadar White House cewa karamin dansa yana "lafiya".


Ana ganin gagarumin taron da aka gudanar a fadar White House yayin da shugaban ke sanar da wadda ya zaba a matsayin alkaliyar kotun kolin kasar ne ya janyo yaduwar cutar.


Tsohuwar mai ba wa Trump shawara Kellyanne Conway da sanatoci biyu na daga cikin mutanen da ke kusa da shugaban da suka kamu.


A ranar 2 ga Oktoba, sa'o'i bayan da ma'auratan farko suka sanar da cewa sun gwada da kyau, shugabar ma'aikatan Misis Trump, Stephanie Grisham ta shaida wa kafar yada labaran Amurka cewa Barron ya yi gwajin mara kyau.


Kusan mutane miliyan takwas ne suka harbu da cutar a Amurka, sannan ta kashe mutane dubu dari biyu da goma sha shidda.



SOURCE: BBCHAUSA

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Barron Trum: Coronavirus ta kama ɗan autan Shugaba Trump"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?