--
Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili



Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirin rushe hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da takwararta ICPC - Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar Buhari a zauren majalisar, mai taken: 


"Dokar hukumar gurbattun kudade" - Sabuwar hukumar za ta tabbata 'yan Nigeria sun amfana da kudaden da aka kwato daga mahandaman kasar, ba tare da boye boye ba A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirin ruguza hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC. 


Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: "Dokar hukumar gurbattun kudade". Ahmad Lawan ya ce sabuwar dokar za ta magance matsalar rufa rufa da ake yi wajen alkinta kudaden da hukumomin biyu ke kwatowa daga barayin kasa.


Buhari a cikin wasikar ya bayyana cewa aikewa majalisar dattijai bukatar rushe hukumomin da samar da sabuwar dokar ya samu sahalewar majalisar zartaswa ta kasa. A cewar wasikar da aka aikata a ranar 6 ga watan Oktoba, sabuwar dokar hukumar zai tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa, safarar kudade ba bisa ka'ida ba da sauran laifuka. 


"Muhimmancin dokar shine kirkirar hukumar yaki da gurbatattun kudade (alkinta kudaden da aka kwato). "Manufofin hukumar shine sa ido kan dokar da kuma yin ruwa da tsaki a alkinta kudaden da aka kwato daga barayin kasa ta hanyar hadin kai da hukumomin tsaro. 


"Sannan abu mai muhimmanci shine, hukumar za ta tabbata 'yan Nigeria sun amfana da kudaden da aka kwato daga mahandaman kasar, ba tare da boye boye ba." 


Idan har aka amince da wannan doka, za ta taimaka wajen dakatar da EFCC da sauran hukumomin yaki da rashawa guda 6 daga rufe asusun mutanen da ake bincika. Sauran hukumomin sun hada da hukumar ICPC, NDLEA, NFIU, NAPTIP, CCB da kuma rundunar 'yan sandan Nigeria," 


a cewar shugaban majalisar dattijan. A shekarar da ta gabata tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ne ya amince da dokar, sai dai tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya nuna rashin amincewa da dokar. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?