--
An kama mutane 12 da ake zargi da kone ofishin 'yan sanda yayin zanga-zanga

An kama mutane 12 da ake zargi da kone ofishin 'yan sanda yayin zanga-zanga


Zangar-zangar lumana da aka fara domin neman a rushe rundunar SARS ta rikide zuwa rikici a sassan Nigeria da suka hada da Abuja - Sakamakon hakan ne babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin baza wasu jami'ai na musamman a fadin kasa 


Ana zargin ma su zanga-zanga da tafka barna, su kuma ma su zanga-zanga na zargin an yi hayar batagari don su bata musu zanga-zanga Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, a ranar Talata, ya bayyana cewa an kama mutane 12 da ake zzargin da hannunsu a kai hari tare da kone wani ofishin 'yan sanda a Benin, jihar Edo. 


A cikin wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda na kasa (FPRO), Mista Frank Mba, ya fitar, ya bayyana cewa an samu bindigu kirar AK47 guda biyar da aka sace daga ofishin da aka lalata. 


IGP Adamu ya bada umarnin gaggauta tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati da na jama'a a fadin kasar nan. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Talata yace shugaban yan sandan ya kuma yi umarni da a tura yan sanda masu yawan gaske zuwa ga cibiyoyin kula da masu laifi da ke fadin Kasar.


Umarnin na zuwa ne biyo bayan karuwar lalata kayayyakin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane da ke faruwa a wasu jihohin kasar da ma birnin tarayya, Abuja. 


"Bugu da kari, kwamishinonin yan sanda a jihohi 36 na Najeriya da birnin tarayya, Abuja, za su yi aiki don ganowa tare da ware ɓata gari daga cikin masu zanga zangar lumana. za a kama masu barna tare da ladabtar gurfanar dasu.


Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "An kama mutane 12 da ake zargi da kone ofishin 'yan sanda yayin zanga-zanga "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?