--
Zargin barazana ga rayuwa: 'Yan Shi'a sunyi wa jarumi Pete Edochie martani

Zargin barazana ga rayuwa: 'Yan Shi'a sunyi wa jarumi Pete Edochie martani


Islamic Movement of Nigeria, da aka fi sani da Shi'a a Najeriya ta ce ba su ji dadin irin yadda jarumi Pete Edochie ya yi a wani fim da ake shirin fitarwa ba


Shugaban sashin watsa labarai na Shia Ibrahim Musa ya ce duk da hakan ba gaskiya bane sunyi barazana ga rayuwarsa domin su masu son zaman lafiya ne 


Ibrahim Musa ya yi ikirarin cewa Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanat Tukur Buratai ne ya dauki nauyin fim din da nufin nunasu  amatsayin masu son tayar da fitina Shugaban sashin watsa labarai na Islamic Movement of Nigeria, Ibrahim Musa ya nesanta kansu daga barazanar kisa 


Jarumi Pete Edochie ya ce ana masa barazana da kisane  saboda fitowa a fim din 'Fatal Arrogance' a matsayin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. 


A hirar da Ibrahim Musa ya yi da Alexander Okere wadda The Punch ta ruwaito ya ce su basu  taba yi wa kowa barazana ba tsawon shekaru 40 da kafuwarsu a Najeriya sai dai sune ake kai wa hari. 


Ya cigaba da cewa ba su gamsu da dalilan da jarumin ya bayar ba na cewa shi aikinsa kawai ya yi a matsayin jarumi amma ba shi ya rubuta fim din ba, 


"A matsayinsa na kwararren jarumi ya kamata ya karanta labarin ya kuma san dalilin yinsa." Har wa yau, ya ce ya ikirarin cewa kowa ya lura da irin tufafin da Edoche ya saka a fim din ya san Sheikh Zakzaky ake kwaikwayo. 


Sannan ya yi ikirarin cewa Shugaban hafsin sojojin kasar Najeriya Laftanar Tukur Buratai ne ya dauki nauyin shirya fim domin sauya abinda ya faru tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a nuna kamar su mutane ne masu son tayar da fitina. 


"Ka duba irin tufafin da suka saka kuma suna zanga-zanga suna ambaton ‘Allahu akbar. La ilaha illallah.’ Haka muke zanga-zanga kamar yadda aka sani." Da aka masa tambaya ko yana da hujjar cewa Buratai ne ya dauki nauyin yin fim din, 


ya ce, "Mun san wanda ya rubuta littafin 'Fatal Attraction' ka duba yadda ya yi kama da 'Fatal Arrogance' kuma dama marubucin mai yi wa sojoji kwangila ne duk cewa suna buya karkashin kungiyoyin jin kai." 


Ibrahim Musa ya ce sun nemi kada a fitar da fim din duba da cewa an bata musu suna cikin fim din kuma idan aka fitar za su garzaya kotu su bi hakinsu. 


Source: legit.ng

DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Zargin barazana ga rayuwa: 'Yan Shi'a sunyi wa jarumi Pete Edochie martani "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?