--
Yanzu-yanzu: Mawakin da yayi batanci ga Annabi ya daukaka kara

Yanzu-yanzu: Mawakin da yayi batanci ga Annabi ya daukaka kara

Yahaya Sharif-Aminu, mawakin da kotun Shari'ar Musulunci ta yankewa hukuncin kisa a jihar kano kan batancin da yayiwa manzon Allah (SAW) ya daukaka kara.

A karar da lauyansa, Kola Alapini, ya shigar ranar Alhamis a babban kotun jihar Kano, Sharrif-Aminu ya ce bai amince da hukuncin kotun shari'ar Musulunci ta yanke ba.

Lauyan ya bayyana cewa dokar Penal Code na 2000 ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma hakkin bil adama.

Gabanin yanzu, lauyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana mata cewa lauyoyi da dama na gudun shiga lamarin Yahaya Sharrif saboda tsoron abinda ka iya biyowa baya musamman jiha irin Kano.

Wani dan rajin kare hakkin yace. "Yawancin lauyoyi masu kare hakkin bil adama a Kano da na bukata su shiga lamari suna ki saboda tsoro."

"Yawancinsu na tsoron matasa na iya kona musu ofishohinsu ko a kai musu hari ko kuma a kashesu don suna kare mai batanci."

Idan za a iya tunawa babban kotun Shari'a da ke Kano ta samu Aminu-Shariff da laifin batanci kuma ya yanke masa hukumcin kisa ta hanyar rataya. A watan Maris ɗin shekarar 2020,

mawaƙin mai shekaru 22 ya rera wata waƙa mai ɗauke da batanci ga Manzon Allah ya tura a dandalin sada zumunta ta WhatsApp, hakan ya sa mutane suka harzuƙa.

Bayan haka, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis ya ce a shirye ya ke ya saka hannu domin a zartar da hukuncin kisar da kotu ta yanke wa mawaƙi Yahaya Sharif-Aminu da ya yi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).

Da ya ke jawabi bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, Ganduje ya ce kotu ta bawa wanda aka yanke wa hukuncin wa'adin kwanaki 30 don ɗaukaka ƙara, idan bai ɗaukaka karar ba shi kuma ba zai bata lokaci wurin rattaba hannu a kan hukuncin ba.

SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: Mawakin da yayi batanci ga Annabi ya daukaka kara "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?