--
Yanzu yanzu: Buhari ya taya Obaseki murnar sake lashe zaben Edo

Yanzu yanzu: Buhari ya taya Obaseki murnar sake lashe zaben Edo


Shugaba Muhammadu Buhari ya taya dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki murnar sake cin zaben jihar 

Buhari, a cikin wata sanarwa daga Bashir Ahmad, ya ce nasarar da Obaseki ya samu, alama ce ta kokarinsa na tabbatar da sahihin zabe a gwamnatinsa 

Legit.ng ta ruwaito maku cewa, hukumar INEC ta sanar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan samun kuri'u 307,955 Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya taya Godwin Obaseki da jam'iyyar PDP murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo, da aka gudanar ranar Asabar 20 ga watan Satumba, 2020. 

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa daga mai tallafa masa ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bukaci Obaseki da ya nuna dattako akan wannan nasara. 

A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, Hukumar zabe INEC ta sanar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan samun kuri'u 307,955.

Shugaban kasa Buhari ya ce, "Kokarina na ganin an gudanar da sahihin zabe ya tabbata, saboda ba don anyi sahihin zabe ba, da bangon siyasa da demokaradiyyar kasarmu ya ruguje." Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Edo a 

karo na biyu bayan ya yi nasarar doke abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC. Wannan shine karo na biyu da Obaseki ke yin nasara a kan Ize-Iyamu, inda a shekarar 2016 ma hakan ta kasance sai dai a lokacin Obaseki ya yi takara a karkashin APC yayin da Ize-Iyamu ke PDP.

INEC ta sanar da cewa Obaseki ya zama zakara ne a zaben gwamnan bayan samun kuri'u mafi rinjaye na 307,955 inda mai biye masa Ize-Iyamu ya samu kuri'u 223,619. 

Wanda ya zo na uku a zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP da kuri'u 323, sai na hudu dan takatar jam'iyyar LP da ya samu kuri'u 267. Hukumar zaben ta ce adadin masu zabe da aka tantance domin kada kuri'a a jihar 557,443, yayin da adadin kuri'u masu sahihanci 537,407. Jimillar kuri'un da masu zabe suka kada 550,242, sannan kuri'un da suka lalace kuma 12,835. 

Jam'iyyu 14 ne suka gabatar da 'yan takara a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu yanzu: Buhari ya taya Obaseki murnar sake lashe zaben Edo "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?