LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Yan sanda sun shawo kan saurayin da ya dauka alwashin kashe kansa idan bai aura Hanan Buhari ba

Wani matashi Abba Ahmad ya haƙura da shirin da ya yi na kashe kansa sakamakon rashin samun damar auren ɗiyar Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan Buhari.

Ahmad ya haƙura ne bayan shawarwari da jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya suka bashi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ahmad, ɗalibin jami'ar Maitama Sule ta Kano (tsohuwar jami'ar North West) ya daɗe yana aika sakon neman Hanan ta aure shi a Facebook da Instagram.

Matashin da mahaifinsa ya rasu tun a shekarar 2013 ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa kyawun Hanan da karatun da ta yi ne ya ke burge shi.

Hanan, mai shekaru 22 ta yi karatu ne a fanin koyon ɗaukan hoto a Jami'ar Ravensbourne da ke Ingila.

"Ina ƙaunar Hanan ne saboda kyawun fuskarta, karatun boko da ta yi da kuma gaskiya irin na mahaifinta (Shugaba Buhari).

"Na yi ƙoƙarin sanar da ita amma ban san ko saƙon ya isa wurin ta ba," in ji Ahmad. Ya rubuta a shafinsa cewa zai kashe kansa idan Hanan ta auri wani namiji daban a ranar Juma'a.

A lokacin da majiyar Legit.ng ta tambayi dalilin da yasa zai kashe kansa saboda mace, ya ce: "Na faɗa ne kawai."

Matar shugaban ƙasa, A'isha Buhari ta wallafa hotunan auren ƴar ta a ranar Juma'a da ake ɗaura a fadar shugaban kasa a Instagram.

An fara bukukuwa kafin auren Hanan da Turad Sha'aban tun a ranar Alhamis 3 ga watan Satumba. Muhammed Turad mashawarci na musamman ne ga Ministan Ayyuka, Babatunde Raji Fashola.

Turad ɗan tsohon ɗan majalisa ne mai wakiltar mazabar Zaria a majalisar wakilai ta tarayya daga 2003 zuwa 2007, Mahmud Sani Sha'aban.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna ya ce bisa umurnin Frank Mba ya gayyaci Ahmad zuwa hedkwatar su inda aka bashi shawarar kada ya kashe kansa.

Kwamishinan ƴan sanda Habu Sani da limamin ƴan sanda duk sun bashi shawarwari.

Kakakin rundunar ƴan sanda na ƙasa, Frank Mba ya yi magana da Ahmad a wayar tarho na tsawon minti 6 da daƙika 6 inda ya bashi shawarar kada ya kashe kansa duk da bai auri yar shugaban ƙasa ba.

An tunatar da shi cewa zai iya auren wata matar ƙyayawa kuma addinin sa ya hana mutum ya kashe kansa.

Bayan ya haƙura, Ahmad ya mika godiyarsa ga yan sandan kuma ya ce yana son ya shiga aikin ɗan sanda saboda yanayi mai kyawu da suka warware masa matsalar da ya shiga.

Kwamishinan ƴan sanda Sani ya bashi shawarar ya siya fom ɗin shiga aikin ɗan sandan idan za a sake ɗaukan sabbi a nan gaba.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments