--
Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun

Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun


Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mutum da ake zargi da yin fim din batsa a wani lambu a jihar Ogun ya kuma watsa a dandalin sada zumunta Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya tafi wani karamin lambu ne a jihar ya kuma nadi bidiyon batsan sanye da kaya na wasu mabiya addinin gargajiya 

Yan sanda sun ce za su gudanar da bincike a kan lamarin kana za su gabatar da wanda ake zargin a kotu idan akwai bukatar hakan Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta damke wani mutum mai suna Tobilola Jolaosho a kan zarginsa da nadar bidiyon batsa a wani karamin lambu da ke Osogbo. 

Jolaosho, wanda aka zarge sa da lalata da wata mata wacce ta bayyana tsirara, ya nadi bidiyon a watan Yulin shekarar nan sannan ya wallafa shi a kafafen sada zumuntar zamani.

A lokacin da The Punch ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar, kakakin rundunar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da kamen Jolaosho.

Ta yi bayanin cewa an kama shi sakamakon korafin da wata kungiyar mabiya addinin gargajiya a jihar Osun ta bada. Akwai yiwuwar Jolaosho zai iya haifar da karantsaye na zaman lafiya a yankin. Kakakin rundunar 'yan sandan ta ce, "

Awosunwon da ke Idinleke a Osogbo ya sanar da 'yan sanda cewa ya ga Tobiloba Isaac Jolaosho yana sanye da wasu kayan gargajiya tare da wata mace tsirara suna bidiyon batsa kuma ya watsa a kafafen sada zumuntar." 

Ta kara da cewa, tuni 'yan sanda suka ziyarci inda lamarin ya faru kuma sun bada tabbacin cewa za su yi bincike tare da gurfanar da wanda ake zargin idan bukatar hakan ta tashi. 

Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?