LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Yan Najeriya biyu 'sun damfari' Bajamushe naira biliyan ɗaya


Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama mutum biyu bisa zargin damfarar wani ɗan ƙasar Jamus yuro miliyan 2.8 - kwatankwacin naira biliyan 1.2 - a cewar rundunar cikin wata sanarwa.


Cikin sanarwar da ta fitar yau Lahadi, an kama Babatunde Adesanya wanda aka fi sani da Teddy mai shekara 50 da kuma Akinpelu Hassan Abass ɗan shekara 41 tare da haɗin gwiwar hukumar 'yan sandan ƙasa da ƙasa ta Interpol.


Ana zargin mutanen ne da damfarar wani wakilin jihar North Rhine-Westphalia ta Jamus mai suna Freiherr Fredrick Von Hahn ta hanyar yi masa alƙawarin samar musu da kayan aikin kiwon lafiya na kare kai daga cutar korona.


Mutanen biyu na aiki ne tare da taimakon wasu abokansu da ke zaune a ƙasar Holland, in ji sanarwar, sannan sun karɓi yuro miliyan biyu da dubu 200 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kayan kan yuro miliyan 14.7.


Sun aikata zambar ne ta hanyar gabatar da kansu a matsayin dillalan kamfanin ILBN Holdings BV da ke ƙasar Holland bayan sun ƙirƙifri kwafin shafin kamfanin na intanet.


Rundunar ta ce nan gaba kaɗan za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.


 Source: Bbhausa


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments