--
Yajin aiki: Tilas ku zo aiki ranar Litinin - FG ga ma'aikata

Yajin aiki: Tilas ku zo aiki ranar Litinin - FG ga ma'aikata


Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan ta suyi watsi da yajin aikin da kungiyar kwadago ta sanar su zo aiki ranar Litinin - Kungiyar kwadagon ta yanke shawarar fara yajin aikin ne domin karin kudin man fetur da lantarki da gwamnati ta yi 


Sanarwar da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Yemi-Esan ta fitar ya ce dukkan ma'aiakata daga mataki na 12 zuwa sama su zo aiki ranar Litinin Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gargadi dukkan ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa sama da wadanda ke muhimman ayyuka 


su tabbatar sun zo aiki duk da yajin aikin da kungiyar kwadago ta sanar da fara yi a ranar Litinin. Saboda annobar cutar korona, an shawarci wasu ma'aikatan gwamnatin su rika aiki daga gidajensu. 


Kungiyoyin kwadago sun sanar da cewa za su fara yajin aikin ranar Litini a kan karin kudin lantarki da na man fetur. Sai dai shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da kwanan watar 25 ga watan Satumban 2020 ta umurci ma'aikata dake zuwa aiki suyi watsi da batun yajin aikin. 


Wani sashi na sanarwar ya ce, "Bayan kirar da kungiyar kwadaga tayi na fara yajin aiki daga ranar Litinin 28 ga watan Satumban 2020, 

\

ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya tana sanar da dukkan ma'aikatan ta cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da kungiyar kwadagon a halin yanzu da nufin warware matsalolin tare da dakatar da yajin aikin da aka yi shirin yi." 


Kazalika, gwamnatin tarayyar ta janyo hankalin ma'aikatan game da umurnin da kotun ma'aikata na kasa ta bayar na hana kungiyoyin kwadagon zuwa yajin aikin. 


Source: Legit.ng

DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Yajin aiki: Tilas ku zo aiki ranar Litinin - FG ga ma'aikata "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?