--
Tsoho Mai Shekara 60 Ya Yi Wa ’Yar Cikinsa Fyade

Tsoho Mai Shekara 60 Ya Yi Wa ’Yar Cikinsa Fyade


Wata kotun majistare da ke zamanta unguwar Iyaganku a birnin Ibadan na Jihar Oyo ta tsare wani tsoho bisa zargin yi wa ’yar cikinsa fyade.


Ana zargin mutumin mai kimanin shekar 60 ya yi wa ’yar tasa fyade ne a cikin dare.

Alkalin kotun, Misis O.A. Akande ta bayar da umarnin tsare shi har zuwa lokacin da ofishin mai shigar da kara na jihar zai mika rahoton bincikensa.

Daga nan ta dage sauraron karar har zuwa 12 ga watan Nuwamba mai zuwa.

’Yar sanda mai shigar da kara Sajent Gbemisola Adedeji ta shaida wa kotun cewa a ranar 31 ga watan Agusta ne da misalin karfe 10 na safe Mista Aboidun zakke wa diyar tasa mai kimanin shekaru 22 ba tare da amincewarta ba.

Gbemisola ta ce laifin ya saba wa Sashe na 357 na kundin dokokin manyan laifuka na jihar Oyo na shekara ta 2000.

Source: Aminiya Daily Trust 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tsoho Mai Shekara 60 Ya Yi Wa ’Yar Cikinsa Fyade"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?