--
Sun mayar da mu ƙaruwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

Sun mayar da mu ƙaruwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

Da yawa daga cikin matasan Najeriya kan tsallaka kasashen ketare domin neman na rufin asiri sakamakon halin rashin aikin yi da jama'a suka tsinci kansu a ciki.

Amma abun takaici shine yadda wannan lamarin ke sa su fadawa hannun mutanen banza. Su kan yi musu dadin baki ta yadda har suke amincewa da su tare da fatan za su cimma burikansu idan har suka tara daga N150,000 zuwa N600,000.

A wasu lokutan, wadannan 'yan damfarar kan yi wa jama'a alkawarin samun aiki bayan sun isa sannan su dauka dawainiyar tafiyarsu.


Su kan dauka alkawarin karbar a kalla rubi uku na kudin da suka kashewa wanda suka kai Turai. Amma kuma abinda ba a sani ba shine, tafiyar kanta ba mai sauki bace kamar yadda ake tsammani.


A lokuta da yawa, wasu kan rasa rayukansu a hamada ko kuma wurin tsallake teku ba tare da sun kai inda suke fatan kaiwa ba. Wadanda suke kaiwa da ransu, suna karewa a Libya inda ake mayar da su karuwai, ballantana mata.


Wasu kan samu sa'a inda gwamnatin tarayya ke dawo da su gida har su bayar da labaran halin da suka shiga. An gano cewa, a kalla mutum 16,000 'yan Najeriya aka dawo da su daga Turai, Libya da sauran kasashen Afrika a cikin shekaru uku da suka gabata.


Da yawa daga cikin wadanda aka dawo da su a kan basu taimakon kudi wanda zai mayar da su gida. Amma kuma, bayan komawarsu gida, 'yan uwa da abokan arziki kan yi murnar ganinsu ne na makonni biyu kacal. Daga nan a kan barsu su ci da kansu.

Bayan dawo da wasu daga kasashen ketare da gwamnati tayi, an samu tattaunawa da wasu inda suka bayyana halin da duka shiga, Vanguard ta ruwaito.

Daya daga cikin wadanda aka dawo da su mai suna Frank Obeahon, ya jinjinawa gwamnatin tarayya ta yadda suka kokarta tare da ceto rayuwarsu. Ya ce hanya daya ta dakile irin wannan hijira shine, samarwa matasa aikin yi.


Babu abinda zai kaisu barin kasar neman na kansu. Obeahon ya ce ikon Allah ne ya dawo da shi daga Libya, kuma yana godiya ga Ubangiji. Wani daga cikin wadanda suka samu dawowa gida ya ce, "Ina farin ciki da na dawo gida domin fara rayuwa mai dadi. Abinda na fuskanta kafin in kai ga kasar Italiya mutuwa ce.


"Na rasa abokai a hamada da teku. Gara in tsaya a kasata komai wuya da rintsi, dadai in tafi wata kasa." Daya daga cikin matan da ta bukaci a boye sunanta kuwa, cewa tayi,


"akwai lokacin da aka dukeni har na suma, kuma aka hana ni abinci na tsawon kwanaki saboda na ki sauraron wasu kattin maza da aka kawo domin lalata da ni."

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Sun mayar da mu ƙaruwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?