--
Shugaba Buhari Zai Ziyarci Kasar Guinea A Gobe Alhamis Duba Dalili Anan

Shugaba Buhari Zai Ziyarci Kasar Guinea A Gobe Alhamis Duba Dalili Anan


Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya kasar Guinea Bissau daga birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 24 ga Satumba domin halartar taron murnar shekaru 47 da samun 'yancin kasar. 


Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a shafin fadar shugaban kasa na manhajar Facebook.


 Ya bayyana cewa shugaban kasan zai hadu da takwarorinsa na kasan Cote d’ Ivoire, Rwanda, Mauritania, Togo da Liberia.


 Yace: "A birnin Bissau, shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar titin da aka sanyawa sunansa domin karramashi."


 "Bayan haka shugaban kasan da sauran shugabannin kasashen da aka gayyata zasu halarci liyafar da shugaban Guinea Bissau, Umaru Sissoco Embalo, ya shirya."


"Shugaban kasan zai samu rakiyar manyan jami'an gwamnati wanda ya hada da ministan harkokin waje, Geofrey Onyeama; ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Mai ritaya); mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno; da dirakta Janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai Abubakar." 


A karshe, Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa zai dawo Najeriya ana kammala taron.


Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Source: Rariya

DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Shugaba Buhari Zai Ziyarci Kasar Guinea A Gobe Alhamis Duba Dalili Anan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?