--
Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda ya yi batanci ga Annabi a Kano

Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda ya yi batanci ga Annabi a Kano


Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Nigeria da ta yafewa mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW) - Majalisar ta ce yin waka ba laifi bane, don haka, yanke hukuncin kisan ya sabawa dokar yancin dan Adam ta kasa da kasa 


Banda Yahaya Aminu Sharif, akwai kotun da ta yankewa wani dan shekaru 13 hukuncin shekaru 10 a gidan kaso, bisa zarginsa da batanci ga Annabi A ranar Litinin, kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Nigeria da ta saki mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW). 


A watan da ya gabata ne wata kotun shari'a a Kano, ta yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa, bayan da ya yi wakar batanci ga Musulunci da Annabi, kuma ya raba a WhatsApp. 


A cikin wata sanarwar hadin guiwa daga kwararrun MDD, sun bayyana cewa "Waka ba laifi bace," kuma suka bayyana cewa tun farko mawakin bai samu kwararrun lauyoyi ba ne. 


Ita ma wata kwararra a hakkokin al'adun bil Adama, Karima Bennoune, ta bayyana cewa, sabawa dokar yancin dan Adam ne yanke hukuncin kisa don an yi waka tare da raba ta a kafofin sadarwa. Ta roki Nigeria da ta janye wannan hukuncin kisan, kana ta tabbatar da tsaron lafiyar mawakin har zuwa lokacin da zai daukaka kara kan hukuncin. 


Fusatattun mutane sun gudanar da zanga zanga bayan da Sherif ya yi wakar, inda suka kona gidan iyayensa a ranar 4 ga watan Maris. Bangaren shari'a na Nigeria na ci gaba da fuskantar suka tun bayan da ta yankewa dan shekaru 13 hukuncin shekaru 10 a gidan kaso, 


bisa zarginsa da batanci ga Annabi a wata muhawara. Shi ma Daraktan kula da gidan tarihin Auschwitz, Omar Farouq, ya bukaci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yafe wa yaron da ya yi batanci ga addini a Kano. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda ya yi batanci ga Annabi a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?