LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Maigadi ya rasu bayan ya sha giya sannan ya kwanta da takunkumin fuska


Wani dattaijon maigadi mai suna Solomon Ade ya rasu bayan da aka zargi ya kwanta bacci da takunkumin fuska a wurin aikinsa da ke yankin Alako a Abeokuta, a jihar Ogun


A ranar Juma'a, 28 ga watan Augusta. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Solomon wanda ya kasance sananne a yankin, ya saba saka takunkumin fuska tun bayan da cutar korona ta bullo. 


Amma kuma, a ranar Juma'a, 28 ga watan Augusta, tsohon mai shekaru 50 ya sha kofunan giyarsa ta gargajiya wacce aka fi sani da Ogogoro sannan ya kwanta bacci. 


Ya kwanta sanye da takunkumin fuska. An ga gawarsa daga bisani amma sanye da takunkumin fuskar, lamarin da yasa aka yi zargin cewa rashin isasshen numfashi ne ya kasheshi. 


Makwabtan da suka shiga gidan da yake gadi domin diban ruwa sun dinga dukan kofar gidan amma Ede bai fito ba domin budewa An gano cewa, hayaniyarsu a kofar gida ce ta sa ubangidan marigayin ya bude kofar domin masu diban ruwan. 


Daga nan sai ya zarce dakin Ede domin duba lafiyarsa. Ya ga kofar a kulle, lamarin da yasa yayi amfani da karfi wurin budeta. A take ya tarar da gawarsa kwance sanye da takunkumin fuska. 


Ubangidan nasa ya kira jama'a wadanda suka taya shi duba shi sannan suka tabbatar da cewa mutuwa yayi. Wata majiyar ta ce, "Amma daga hayaniyar da jama'a masu diban ruwan ke yi, babu wanda zai yi tsammanin cewa wani mugun abu ya faru. 


"Bayan da maigadin bai bude kofar bane ubangidansa ya fito har ya duba shi sannan ya gane cewa mutuwa yayi." Cike da firgicin abinda ya faru, ubangidan mamacin ya kai rahoto ofishin 'yan sandan yankin Kemta da ke Idi Aba. 


Mazauna yankin sun yi ikirarin cewa, mamacin ya saba shan giya tun bayan da yayi fama da wata damuwa. Maigidan ya ja kunnensa a kan ya kiyaye shan giyar da yake yi. 


"Ya saba cire takunkumin fuska kafin ya kwanta. Amma da ya sha giyar mai yawa da yammacin nan, sai ya kasa. Wadanda suka gan shi da yammacin sun tunatar da shi a kan ya cire takunkumin fuska kafin ya kwanta. 


"Amma kuma, sai ya kwanta ba tare da ya cire ba. Akwai yuwuwar rashin numfashi ne ya kasheshi," daya daga cikin mazauna yankin ya sanar. 


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments