LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Magidancin da ke lalata da 'ya'yansa 4 mata ya ce ubangiji ya halasta mishi hakan

Wata kotun majistare ta gurfanar da wani dattijo mai shekaru 64 a duniya sakamakon lalata da yake yi da 'ya'yansa mata hudu -

Ana zargin Archibong da laifin lalata da 'ya'yansa mata hudu inda yake tsoratar da su da yunwa idan basu amince ba -

Ya sanar da su cewa a littafin bibul, Luth yana saduwa da 'ya'yansa mata hudu kuma ubangiji bai yi fushi da shi ba Wani dattijo mai shekaru 64 mai suna Bassey Archibong da ke gida mai lamba 10 a titin Dipo, yankin Owutu da ke Ikorodu a jihar Legas

ya gurfana a gaban kotu. Ana zargin Archibong da laifin yi wa 'ya'yansa mata har hudu fyade masu shekaru 12 zuwa 20 a duniya, Vanguard ta wallafa.

An gano cewa Archibong ya saba ma'amala muguwa da 'ya'yansa mata tun a 2016. An gurfanar da shi a kan laifuka uku da suka hada da lalata da 'ya'yansa a gaban wata kotun majistare da ke Legas.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su. Dan sanda mai gabatar da kara, John Iberedem, ya ce Archibong yana amfani da abinci wurin jan ra'ayin yaran domin ya yi lalata da su.

Iberedem ya ce, a duk lokacin da yaran suka ki amincewa da shi, ya kan janyo musu ayoyi daga bibul inda Luth yake mu'amala da 'ya'yansa mata kuma Ubangiji bai ladabtar da shi ba. Iberedem ya ce wannan laifin ya ci karo da sashi na 265 sakin layi biyu na dokokin jihar Legas na 2019.

Ya ce, "Wanda ke kare kansa yana dukan 'ya'yansa sannan ya hana su abinci a duk lokacin da suka tambayeshi dalilin da yasa yake lalata da su.

"Yana sanar da su cewa lalata tsakanin 'ya'ya da mahaifinsu ba komai bane, ubangiji ya amince da hakan. "Ya sanar da yaran cewa ubangiji zai kona su matukar suka ki amincewa da shi, kuma ba zai taba ladabtar da shi ba domin ya kusancesu."

Alkalin kotun, F. A Azeez, ya bada umarnin cigaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari har zuwa ranar 30 ga watan Oktoba da za a ci gaba da sauraron karar. A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama masu fyade har mutum 140 a jihar.


Kwamishinan 'yan sanda na jihar Sanusi Buba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis lokacin da yayi hira da su.

Ya ce an kama masu laifin a kararraki 87 da aka kai cikin kananan hukumomi 34 na fadin jihar. Kwamishinan ya ce an dauki wadannan rahotanni nasu ne a cikin tsakiyar wannan shekarar.


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments