LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Luiz Suarez ya amince da komawa kungiyar Juventus

Kungiyar zakarun gasar Serie A Juventus ta zabi Luiz Suarez a matsayin gwarzon dan wasan da zi taimaka mata wurin zira kwallaye. Dan wasan Uruguay din zai cika shekaru 34 a wannan kakar kuma kocin Barcelona Ronald Koeman ya bayyana mai ce baya cikin tsarin shi.


Manema labarai na Gazzetta Dello Sport da kuma Corriere Dello Sport sun bayyana cewa kungiyar Juventus da Luiz Suarez sun kammala yarjejeniya akan komawar dan wasan gasar Serie A. Sharuddan gwanatin Italiya zai taikamawa Juventus ta samu rangwame har na tsawon shekaru biyu wurin biyan Luiz Suarez albashi.


Gwamnatin kasar Italiyan ta saka wannan dokar ne domin ta taimakawa kasar bakidaya bayan annobar korona ta dakile wasu hanyoyin samun kudade a fadin duniya. Tauraron dan wasan har ya tattauna da shugaban Juventus Pavel akan komawar shi italiya a cewar wasu rahotanni.


Shima majan Juve Andrea Pirlo ya tattauna da Suarez ta waya domin siyan dan wasan yazo masu da sauki, kuma idan har Luiz ya koma Juvebtus to zai zamo dan wasa mai nasara wanda yayi aiki tare da zakarun yan wasan duniya Messi da Ronaldo. Kuma shima Pirlo zai hada gagarumar tawaga tare da Dybala,Ronaldo da kuma Suarez.

Source: Hutudole

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments