--
KAICO: Mai gidan Haya ya kashe 'yar haya saboda N11,000

KAICO: Mai gidan Haya ya kashe 'yar haya saboda N11,000


Wani mai gida ya kona yar hayarsa saboda yana bin ta bashin N11,000 daga cikin kudin haya - Mai gidan ya tambayi cikon kudinsa ne amma ta ce masa ya bata kwana daya ta sayar da kifi sannan ta bashi 


Ya bari ta shiga bandaki wanka ya zuba fetur a dakinta da ta dawo kuma ya kuna wuta ya rufe kofa har sai da ta mutu An kama wani mai gidan haya, David Ntiero Okon saboda banka wa yar hayarsa wuta a Calabar, jihar Cross Rivers saboda ta gaza biyan kudin haya N11,000. 


Abin ya faru ne a ranar Laraba a gida mai lamba 9, Ansa Ewa Street a garin Cobham da ke Bayside a Calabar ta Kudu kamar yadda The Punch ta ruwaito.


Rahotanni sun ce mai gidan ya zuba fetur a dakin Misis Mary Samuel sannan ya kuna wuta wadda ya yi sanadin konewar dakin na matar da kayan da ke ciki. Wani ganau da mai gadi da ke zaune a gidan hayan da ya ce sunansa Obongette ya Mary na wacce ta yi kimanin shekaru bakwai a gidan hayar ta kasa biyan mai gidan bashin N11,000 ne saboda hare-haren da masu tada kayan baya ke kaiwa wurin sana'ar ta na sayar da kifi. 


Ya ce, "A ranar Laraba matar ta dawo daga siyo kifi a Oron da ke jihar Akwa Ibom da yamma sai mai gidan ya ce ta biya shi cikon bashin N11,000 na kudin haya da ya ke binta. Ta fada masa bata da kudi a lokacin amma ya bari idan ta sayar da kifin za ta biya. Obongette ya kara da cewa, "Rokon alfarmar da matar ta yi ya fusata mai gidan inda yace bata son biyan kudin ne. 


Da matar ta tafi bandaki yin wanka, mai gidan ya zuba fetur a dakin ta. Bayan ta fito wanka ta shiga aki sai ya kuna wutar ta mamaye dakin. "A lokacin da matar ta yi kokarin fitowa daga dakin, mutum ya rufe kofar ya kuma dako adda ya rika korar mutanen da suka yi yunkurin kawo mata dauki yana barazanar zai kashe su." 


Ya ce bayan matar ta mutu, mutanen unguwar taru suka dauki gawar ta suka kai gidan mai gidan hayar suka ajiye. "A jiya (Alhamis) 'yan sanda sun zo sun kama mutumin sun dauke gawar domin mutumin ya yi yunkurin tserewa amma mutane sun hana shi guduwa. 


Mahaifinsa ne ya gina gidan," in ji Obongette. Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kara da cewa an kama mai gidan an kuma kai gawar wurin ajiya a asibiti. Ta ce, "Ana bincike domin gano ainihin abinda ya faru." 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "KAICO: Mai gidan Haya ya kashe 'yar haya saboda N11,000 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?