--
Kada UNICEF Ta Yi Mana Shisshigi -Gwamnatin Kano

Kada UNICEF Ta Yi Mana Shisshigi -Gwamnatin Kano


Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya ce kuskure ne Hukumar Kula Hakkokin Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi katsalandan a hukuncin daurin shekara 10 da kotu yanke wa wanda ya yi batanci ga Allah.


Babban Jami’in UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins, ya bukaci gwamnatocin jihar Kano da ta Tarayya su gaggauta sanyawa a sauya hukuncin.


Ya ce “Daurin shekara 10 da kotun ta yi wa yaron dan shekara 13, Omar Farouk, ya saba wa hakkokin yara da adalci a Najeriya kamar yadda ita gwamnatin jihar Kano ta aminta.”


A nashi martanin, Kwamishinan Shari’ar Kano ya ce, babu gaskiya a cewar mai laifin karamin yaro ne, saboda abin da ke kan takardar shigar da kara kotun ta nuna cewa shekarunsa 17.


“Saboda haka, cewar Gwamnatin Kano ta shiga maganar bai taso ba, don babu watan kasa a duniya da gwamnatin ta ke katsalandan a hukunci kotu.


“In dai kotu ta yanke hukunci, hanyar kadai da za a bi wajen canja hukuncin shi ne wanda hukuncin bai yi masa ba ya daukaka kara”, inji shi.


Ya ce idan har shekarun mai laifin ba su kai 17 ba kamar yadda takardar shigar da karar ta kumsa, yana da damar daukaka kara daga matakin Babbar Kotun zuwa Kotun Daukaka Kara, har zuwa Kotun koli.


Ya kuma ce a doka ba a yanke ba a yanke wa karamin yaro hukunci musamman na munyan laifuka. Saboda haka bai dace UNICEF ta ce gwamnatin Kano ta shiga ba.


“Ko kasashen turawa da Amurka ba sa katsalandan a hukuncin kotu.


“Da zarar an yanke hukunci ana ba da damar daukaka kara.


“Na san ya daukaka kara, don haka kamata ya yi a jira hukunci kotun da ya shigar da karar”, kamar yadda ya ce.


Idan ba a manta ba, a ranar 10 ga watan Agusta ce Kotun Shari’ar Muslunci ta yanke wa Farouk hukuncin daurin shekara 10 a gidan jarun bayan amsa laifin batanci ga Allah yayin gardama da suka yi ranar 4 ga watan Maris.


Alkalin kotun, Khadi Muhammad Ali-Kani, ya ce laifin Farouk ya saba wa dokar addinin Muslunci, kuma ya yanke masa hukuncin shekara 10 a gidan yari kamar yadda Sashe na 382 (b) na dokar ta tanada.


Ya kuma ba shi tsawon kwanaki 30 na daukaka kara, in har yana bukatar yin hakan.


Source: Aminiya Daily Trust 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kada UNICEF Ta Yi Mana Shisshigi -Gwamnatin Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?