LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Femi Falana SAN ya sa an karbo takardu, zai daukaka kara a shari’ar Aminu Shariff

Ana kokarin daukaka karar Yahaya Aminu Shariff zuwa gaban babban kotu - Kotu ta samu Yahaya Aminu Shariff da laifin cin mutuncin musulunci a baya

Wannan ya sa Alkalin karamin kotun shari’a ya yanke masa hukuncin kisa Ana kishin-kishin din cewa shahararren lauyan nan, Femi Fakana SAN, zai tsayawa Yahaya Aminu Shariff wanda aka yankewa hukucin kisan-kai.

Babban Lauyan zai kare wannan matashi mai shekaru 22 da haihuwa da Alkali ya samu da laifin cin mutuncin addinin musulunci a jihar Kano kwanakin baya. Rahotannin da su ke zuwa mana a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, 2020, sun bayyana cewa Femi Falana ya samu karbar takardun.

wannan shari’a da ake yi. Hakan na zuwa ne makonni uku da samun Aminu Shariff da laifi a gaban wani kotun shari’a. Falana zai tsaya wajen ganin an daukaka kara domin a saki matashin.

Mai magana da yawun bakin bangaren shari’a na jihar Kano, Babajido Ibrahim, ya sanar da manema labarai wannan cigaba da aka samu a shari'ar dazu da rana.

Mista Babajido Ibrahim ya ce takardun wannan kara da zaman kotun da aka yi sun kai ga Femi Falana, a madadin wani Lauya da ya aiko ya wakilce sa a jihar Kano. An gabatarwa wakilin Femi Falana SAN wadannan takardu ne a ranar 2 ga watan Satumba.

Wannan zai bada damar lauyan ya kare wanda ake tuhuma a gaban kuliya. Falana wanda ya yi fice wajen kare hakkin Bil Adama, zai duba hukuncin da Alkalin kotu ya yanke a watan Agusta, daga nan ya garzaya kotu, ya daukaka wannan shari’a.

Wannan shari’a ta jawo ce-ce-ku-ce har a ketare, inda wasu su ke ganin bai kamata a yankewa mutum hukuncin kisa a kasar da kowa ya ke da ‘yancin yin magana ba. A gefe guda, masana addinin musulunci sun yaba da hukuncin da Khadi Aliyu Muhammad na kotun shari’a da ke Hausawa ya yi, sun ce haka addinin musulunci ya tanada.

SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments