--
El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili

El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili


Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta yi watsi da rahoton 'yan majalisar nadin sarakuna a masarautar Zazzau 


Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana zarginsu da karbar cin hanci daga daya daga cikin masu zawarcin karagar 


A halin yanzu gwamnan ya buakci dukkan masu bukatar kujerar su fito domin sabunta tantancewa daga jami'an tsaro 


Gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin Zazzau, 


wata majiya da ta san kan lamrin ta tabbatar wa da Premium Times. 


Wannan hukuncin ya dawo da Ahmed Bamalli, wanda aka tabbatar da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ke so a cikin masu zawarcin karagar mulkin. 


Premium Times ta gano cewa, gwamnan ya yanke wannan hukuncin bayan zargin da yayi an bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar cin hanci. 


A farkon makon nan ne aka gano cewa, 'yan gidajen sarautu hudu ne daga gidaje uku na sarautar Zazzau suka fito neman kujerar. 


Sun hada da Iyan Zazzau, Bashir Aminu; Magajin Garin Zazzau, Ahmed Bamalli; Yeriman Zazzau, Munir Ja’afaru da Turakin Zazzau, Aminu Idris. 


Daga cikin mutum hudun, 'yan majalisar sun mika sunayen mutane uku inda Ahmed Bamalli bai samu shiga ba. 



Wata majiya daga fadar ta tabbatar da cewa, sunan Ahmed Bamalli bai shiga jerin bane saboda hatta kakansa bai yi sarautar Zazzau ba. 


Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewa, daya daga cikin masu neman kujerar ya bai wa 'yan majalisar cin hanci kafin su mika rahoton gaban gwamnan. 



Hakan ce ta sa gwamnan ya yi kira ga dukkan masu neman karagar da su dawo a sake sabuwar tantancewa. 


Jimillar masu neman kujerar sun kai mutum 11 kuma an samo sabuwar hanyar tantacewa wacce jami'an tsaro ce za su yi. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 


0 Response to "El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?