--
Duba Mutane Biyar Da Daya Acikinsu ka'iya Zama Sabon Sarkin Zazzau

Duba Mutane Biyar Da Daya Acikinsu ka'iya Zama Sabon Sarkin Zazzau


Hankalin ƴan Najeriya musamman arewacin ƙasar na dakon sanarwar sabon sarkin Zazzau da zai gaji Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris.



A ranar Lahadi ne Allah Ya yi wa mai Martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa bayan shafe shekaru 45 kan gadon sarautar Zazzau.


Marigayin wanda shi ne sarkin Zazzau na 18, ya rasu ne yana da shekara 85 a duniya.


Bisa tsarin sarautar Zazzau ana zaɓen sabon sarki ne daga gidajen masarautar guda huɗu - wato daga Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Katsinawa da kuma Gidan Sulluɓawa.



Masanin tarihin masarautar Zazzau kuma daraktan gidan Tarihi na Arewa da ke ƙarƙashin Jami'ar Ahmadu Bello, Shu'aibu Shehu Aliyu ya shaida wa BBC cewa waɗannan gidajen ne ke turo ɗan takara ɗaya da zai nemi sarautar Zazzau ga masu zaɓen sabon sarki.



Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ne zai zaɓi sabon Sarkin Zazzau, cikin mutum uku daga cikin ƴaƴan gidan masarautar Zazzau da masu naɗin sabon sarki suka tura masa.


Mutum biyar daga cikin waɗannan gidajen da ake ganin cikinsu za a zaɓi sabon sarkin Zazzau na 19, sun haɗa da:



1, Turakin Zazzau - Aminu Shehu Idris


Aminu Shehu Idris ya fito ne daga gidan Katsinawa, Gidan Malam Idris Auta. Shi ne babban ɗan margayi Alhaji Shehu Idris.


Shi yake riƙe da sarautar Turakin Zazzau a yanzu.


Turakin Zazzau wanda ma'aikaci ne a kamfanin mai na NNPC, ƙwararre ne a harakar kasuwar fetur da gas a Najeriya.


Kasancewarsa babban ɗan marigayi Alhaji Shehu Idris, ana ganin yana iya zama sabon sarkin Zazzau.


2, Yariman Zazzau - Mannir Jafaru


Yana iya zama sabon sarkin Zazzau saboda girmama shi da ake da kuma sanayyar da yake da ita ko ba don ma sarautarsa ta Yariman Zazzau ba.


Yariman Zazzau Mannir Jafaru tsohon shugaban hukumar NIMASA ne kuma tsohon kwamishina ne a jihar Kaduna.


Mannir Jafaru, ya fito ne daga gidan Barebari, kuma ɗan tsohon sarkin Zazzau ne Malam Jafaru Ɗan Isiyaku wanda ya yi sarki daga 1937 zuwa 1959.


Wasu na ganin wannan wata dama ce ga Yariman ya gaji mahaifinsa.


3, Magajin Garin Zazzau - Ahmad Nuhu Bamalli


Ahmad Nuhu Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa, kuma shi ne yanzu Magajin Garin Zazzau, babbar sarauta a Masarautar Zazzau.


Ambasada Ahmad jika ne ga Nuhu Bamalli tsohon Magajin Garin Zazzau kuma tsohon minista a Najeriya.


Magajin garin Zazzau wanda masani shari'a ne da diflomasiyya shi ne jekadan Najeriya a Thailand a yanzu.


Saboda girman sarautarsa ta Magajin Garin Zazzau da kuma kusancinsa da gwamnati ana ganin zai iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.


4, Iyan Zazzau - Bashir Aminu


Iyan Zazzau Bashir Aminu ya fito ne daga gidan Katsinawa ɗan tsohon Sarkin Zazzau na 17 Malam Muhammadu Aminu.


Iyan Zazzau ya taɓa rike sarautar Dan Madamin Zazzau kafin ya zama Hakimin Sabon Gari.


Bashir Aminu ana ganin yana iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.


5, Shitu Ibrahim Dikko - Dangaladiman Wazirin Zazzau


Dangaladiman Wazirin Zazzau Hakimin Gundumar Gabasawa Alhaji Shitu Ibrahim Dikko ya fito ne daga gidan Sulluɓawa ɗaya daga cikin gidajen da ke da gadon sarautar Zazzau.


Dangaladiman Wazirin Zazzau ɗaya daga cikin jikokin Sarkin Zazzau ne marigayi Malam Abdussalam daga gidan Sulluɓawa wanda ya yi mulki tsawon shekara huɗu tsakanin 1853 zuwa 1857.


A 2008 marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya ba shi sarautar Dangaladiman Wazirin Zazzau kuma gwamnan Kaduna Malam Nasir El- Rufa'i ya naɗa shi Hakimin Gabasawa a yankin Kaduna ta Arewa a 2018.


Kasancewarsa daga gidan Sulluɓawa ana ganin yana iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.


Masu zaɓen sabon Sarkin Zazzau

Masanin tarihin masarautar Zazzau kuma daraktan gidan Tarihi na Arewa da ke ƙarƙashin Jami'ar Ahmadu Bello, Shu'aibu Shehu Aliyu ya ce majalisar masu zaɓen sarkin Zazzau ta ƙunshi mutum biyar.


Su za su zauna su tantance waɗanda suka cancanta daga nan su tura wa gwamnan jihar Kaduna sunayen mutum uku domin ya zaɓi ɗaya a matsayin sabon sarki. Don haka sai abin da gwamna ya yanke.


 Masanin ya ce masu zaɓen sabon sarkin sun haɗa da Makaman Zazzau, Alhaji Muhammad Abbas da Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Limamin Kona Sheikh Muhammad Sani Aliyu da kuma Limamin Gari, Sheikh Dalhatu Ƙasim.


Daga Comr Abba Sani Pantami

Source: Rariya 


DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Duba Mutane Biyar Da Daya Acikinsu ka'iya Zama Sabon Sarkin Zazzau"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?