--
Duba Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai

Duba Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai


Bawada Audu mai shekaru 50 a duniya ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi - Ana zarginsa da laifin birne jinjirin jikansa da rai a bayan gidansa har ya mutu 


An gano cewa diyarsa mai shekaru 17 ce ta haifesa bayan cikin shegen da ta dauka a shekarar nan Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke wani mutum mai suna Bawada Audi mai shekaru 50 a duniya, a kan kashe jaririn jikansa a Rimin Ziyam da ke karamar hukumar Toro ta jihar. 


Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmed Wakili, wanda ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba, ya ce bayan diyar wanda ake zargin mai shekaru 17 ta haihu, ya kwace jaririn inda ya birnesa. 



Bawada Audu ya kwace jaririn diyarsa mai suna Hafsat bayan haihuwar da tayi sannan ya birnesa da ransa a bayan gidanshi. "A ranar 16 ga watan Satumban 2020 wurin karfe 8 na dare, rundunar hadin guiwa tsakanin 'yan sanda da masu rajin kare hakkin dan Adam sun kawo wata budurwa. 


"Yarinyar mai shekaru 17 a duniya da ke zama a Rimin Zayam a karamar hukumar Toro ta Bauchi ta ce mahaifinta ya kwace mata jinjirinta bayan ta haihu sannan ya birnesa da ransa," takardar tace. 



Bayan samun rahoton, an hako jinjirin kuma an gaggauta mika shi babban asibitin yankin inda aka tabbatar da cewa ya rasu, shafin Linda Ikeji ya wallafa. 


Kakakin rundunar 'yan sanda ya kara da cewa, "Bugu da kari, Hafsat ta sanar da cewa wani Danjuma Malam Uba da ke gidansu ya yi mata fyade a 2020, amma ya yi batan dabo. "An bai wa dagacin kauyen gawar jinjirin yayin da aka damke wanda ake zargi kuma ya amsa laifinsa." 


Source: Legit.ng

DAGA: 

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Duba Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?