--
Batanci Ga Annabi: Falana Ya Yi Karar Gwamnati Najeriya A Hukumar Kare Hakkin Dan Adam

Batanci Ga Annabi: Falana Ya Yi Karar Gwamnati Najeriya A Hukumar Kare Hakkin Dan Adam


Bayan daukaka karar mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi (SAW), Femi Falana ya yi karar Gwamnatin jihar Kano da ta Tarayya a gaban Hukumar kare hakkin bil’adama ta Afrika da ke Banjul, babban birnin kasar Gambia.

Falana wanda babban lauya ne kuma me rajin kare hakkin bil’adama, bayan daukaka karar hukuncin da aka yankewa Sharif Yahaya Sharif, matashin da aka kama da laifi batanci ga Manzon Tsira Annabi (SAW) a Kano, ya kuma kai karar Gwamnatin jihar da ta Tarayya har gaban Hukumar kare hakkin bil Adama da ke makociyar kasar.

Bajimin lauyan yana neman Hukumar ta yi amfani da ikonta kamar yadda sashe na 100 sakin layi na daya cikin dokokinta ya bata dama.

Falana a sakon da ya aika mai dauke da kwanan watan ranar 8 ga watan Satumba, ya nemi hukumar da ta shiga lamarin saboda a cewarsa an dannewa matashin hakkinsa yayin da ake neman zartar masa da hukuncin kisa.

“Na rubuto muku wannan takarda a madadin Sharif Yahaya Sharif don neman Hukumar ta yi la’akari da wannan bukata cikin gaggawa.”

“Na gabatar muku da bukatar ne tare da isar da sako a madadin Sharif Yahaya Sharifa wanda ake yanke masa hukuncin kisa saboda aikata sabo a jihar Kano ta Najeriya.”

Fitaccen lauyan ya ce duk da an daukaka kara amma muddin hukumar ba ta yi gaggawar shiga lamarin ba, to kuwa babu tabbacin za a yi wa matashin adalci domin babu wata alama da ke nuna za a fasa zartar da wannan hukunci.

Aminiya Daily Trust


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Batanci Ga Annabi: Falana Ya Yi Karar Gwamnati Najeriya A Hukumar Kare Hakkin Dan Adam"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?