LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

KAI TSAYE DAGA EDO: An Ba Hamata Iska A Zaben Gwamnan Edo- {Kalli Bidiyoyi Da Hotuna}

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa kai-tsaye a zaben Gwamnan Jihar Edo na yau 19 ga Satumba, 2020. 

Wakilanmu a Jihar da dalibai da cibiyar PTCIJ ta horas kan binciken kwakwaf za su rika aiko da bayanai da hotuna da za mu rika wallafawa akai-aika saboda ku san wainar irin da ake toyawa a zaben. Za ku iya zuwa kasan wanna shafin domin karanto yadda abubuwan ke gudana tun da farko. A kasance tare da mu.


Zabe na gudana cikin lumana.

Da misalin 10:30 na safe, a Rumfa ta 13 zuwa 13 a Mazaba ta 5 da ke Kwalejin Marie Goretti, Karamar Hukumar Ikpoba/Okha, ana tantance masu zabe tare da jefa kuri’a a lokaci guda ba tare da wata matsala ba.


Masu zabe sun ba wa jam’ian INEC hadin kai wurin kiyaye dokokin kariyar COVID-19.


Wakilan jam’iyyu na yi wa tsofaffi zabe


Ana zargin jami’an manyan jam’iyyu da yin amfani da yatsun tsoffin mata da zuka zo zaben wajen dangwala wa jam’iyyunsu kuri’a a Maternitiy, Imiomime, Okpella III, Karamar hukumar Etsako ta Gabas.Fada ya kaure a rumfar zabe

10:48 na safe an ba hamata iska a Makarantar Firamare ta Ologhe, da ke Ebelle, Mazaba ta 06, Rumfa ta 07, Karamar Hukumar Igueben.Hatsaniya a rumfar zaben Gwamna Obaseki


Rahotanni sun ce an samu ‘yar takaddama a rumfar zaben da Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya je ya jefa kuri’a.


Tun da sanyin safiya jami’an zabe da sauran jama’a suka yi ta dakon zuwan gwamnan, wanda ya isa wurin bayan karfe 10.20.


Da zuwa gwamnan ya je ya wanke hannunsa bisa tsarin kariyar COVID-19 kafin ya zarce a tantance shi.


Jami’an tsaro sun samu nasarar kwantar da hankalin jama’a kuma komai ya ci gaba yadda ake bukata.


Dan takarar APC Ize-Iyamu ya jefa kuri’arsa

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar Edo, Osagie Ize- Iyamu ya kada kuri’arsa a mazaba ta 4, rumfa ta 26 da ke Iguododo a Karamar Hukumar Orhiomwon.


Ize-Iyamu ya ce cewa ya ga kamar mata ba su fita sosai ba, yana kyautata zaton matan da za su fito su kada kuri’a za su fi maza yawa.


Ya ce yana da kwarin gwiwar samun nasara zaben


Bayan kada kuri’arsa dan takarar ya yaba da yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) ke gudanar da zaben cikin lumana’ da kuma kiyaye dokokin kariyar COVID-19.


“Muna ba mutane kwarin giwa su fito rukuni-rukuni domin bin ka’idojin COVID-19 na bayar da tazara”, inji shi, bayan ya yi zabenGwamna Obaseki ya kada kuri’arsa

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya jefa kuri’arsa a zaben da yake neman wa’adin mulki na biyu karkashin inuwar jam’iyyar PDP inda yake fafatawa da babban da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu.


Obaseki ya jefa kuri’arsa ce a Makarantar Firamare ta Model Emokpae da ke birnin Benin.Gwamna Godwin Obaseki a rumfar zaben da ya jefa kuri’a


Ba a bar nakasassu a baya ba

Malam Yakubu Muhammad da Halima masu fama da lalurar ido sun fito domin su jefa kuri’a a makarantar firamare ta Model da ke Emokpae, Benin.An yi wa nakasassu da tsofaffi tanadi.

An ba wa tsofaffi da nakasassu kulawa ta musamman sannan aka kebe musu wurin zama domin saukaka musu bin layin zabe a mazaba ta 5, Karamar Hukumar Etsako ta Tsakiya.Kayan zabe sun isa da wuri

8:25 na safe jami’an zaben suka lika jerin sunayen masu zabe, minti biyar kafin lokacin fara zaben a mazaba ta 11 rumfa da 5 (Uzairue ta Kudu maso Yamma) a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma (PTCIJ).Dattawa sun fito da karfinsu

Tsofaffi sun fito da kwarin gwiwarsu domin jefa kuri’a a zaben na yau.


An ga wasunsu sun zauna tare da juna a Rumfa ta 8, Mazaba ta 6 da ke Makarantar Firamare ta Egure, Karamar Hukumar Igueben.


Tuni aka bari dattawan su jefa kuri’a a rumfar inda komai na tafiya cikin lumana.akardar sakamakon zabe ta yi batar dabo

Masu zabe sun yi bore bayan takardar rubuta sakamakon ta yi batar dabo bayan an kammala rattaba hannu a kanta a mazaba ta 4, rumfa ta 2, Karamar Hukumar Owan ta Yamma, da misalin karfe 8.53 na safe.


Masu zaben na nuna bacin rai saboda abin da suka kira ko-in-kula da baturen rumfar zaben ya nuna (PTCIJ).


Kariyar COVID-19

Masu zabe da jami’ai na bin matakan kariyar COVID-19 a wasu daga rumfunan zaben da wakilan namu suka ziyarta.


Mutane na bayar da tazara tsakaninsu a kan layin zabe, suna sanye da takunkumi sannan akan wanke hannu kanfin a kai ga zuwa a tantance mutum.


Kazalika akan yi feshin magani a kan jerin sunayen masu zaben domin tabbatar da kariyar cutar.


An fara jefa kuri’a a wasu wurare 

An fara zaben a mazaba ta 9, rumfa ta 10 mai masu zaben 1191 a Karamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas, da misalin karfe 8.59 da safe (PTCIJ).Da misalin 8:45 na safe aka fara tantance masu zabe a Rumfa ta 3, Mazaba ta 2 a Karamar Hukumar Ovia ta Yamma.


Wasu ba su ga sunayensu ba

Baturen zaben rumfar zabe ta 10, mazaba ta 11 a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma ya yi wa jerin sunayen masu zabe feshin magani domin kariya daga cutar coronavirus.


AN tuntube shi game da wadanda ba su ga sunayensu a cikin jerin sunayen da aka lika ba, amma ya ce babu abin da za a iya yi a akai. (TPCIJ).


Tun da sassafe jama’a suka fita

Tun da sanyin safiya jama’a a sassan Jihar Edo suka yi ta fita domin zuwa rumfunan zabe.


Jami’an zabe, da suka hada da masu yi wa kasa hidima da wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro da masu sa ido sun yi cincirindo a cibiyoyin hukumar zabe (INEC) da ke Jihar Edo domin rabon kayan zabe da kai su rumfunan da za a gudanar da zaben da wuri.


Tuni dai kayan zaben suka fara isa rumfunan zabe.


Mista John Inadehi mai shekara 83 ya fito domin jefa kuri’a a garin BeninMista John Inadehi mai shekara 83 ya yi zabe fiye da sau 20.


Ya ce yanzu ma a shirke yake ya jefa kuri’arsa kuma ba shi da wata fargabar cewa za a yi murdiya.“Ni dan birnin Benin ne kuma mu ba ma tashin hankali. Ina da kwarin gwiwar cewa za a gudanar da sahihin zabe,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.


Ba za a bar mu a baya ba

Duk da rufe ayyuka da a aka yi domin gudanar da zaben, masu muhimman sana’oi, irin su Joy, mai sayar da abinci a babban titin Ring Road na birnin Benin, sun fito domin su jefi tsuntsu biyu da dutse guda.‘Yan kasuwa da ‘yan tireda sun rufe shagunansu kamar yadda hukumomi suka umarta a ranar zaben.


Sallama!


Muna muku barka da safiya a wannan shafin da zai rika kawo muku abin da ke faruwa a zaben Gwamnan Jihar Edo na 19 ga Satumba, 2020 kai-tsaye.


Wakilanmu za su rika aiko da bayanai akai-aika domin ku san yadda ake ciki.


Dalibai masu koyon aikin jarida da Cibiyar Koyar da Binciken Kwakwaf a Aikin Jarida ta Premium Times (PTCIJ) ta horas domin kawo rahotannin zaben daga da Mazabun Majalisar Dattawa uku da ke jihar Edo za su mara wa wakilan namu baya.


Za ku iya amfani da maudu’an #EdoDecides, #EdoElects ko kuma #DTEdoGuber domin bin labarun zaben.


A kasance tare da mu.

Source: Aminiya Daily Trust


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments