LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Alkawari ya cika, an daura auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban (Kalli Hotuna)

Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Hanan Buhari, ta tabbata matar Muhammad Turad Sha'aban - Tuni hotunan bikin 'yan gatan ya karade kafofin sada zumuntar zamani.

Mahaifiyar amarya, Aisha Buhari, cike da farin ciki ta wallafa hotunan ango da amaryar a shafinta na Instagram Babu shakka ranar 4 ga watan Satumban 2020 babbar rana ce ga iyalan shugaban kasa Najeriya, Muhammadu Buhari.

Sun mika auren diyarsu a fadar shugaban kasar Najeriya da ke fadar Aso Rock a Abuja. Tuni sakonnin sam barka da taya murna ya karade kafofin sada zumuntar zamani ga Hanan Buhari da kyakyawan angonta, Muhammad Turad Sha'aban, a yayin da suka zama mata da miji.


A post shared by H.E Mrs Aisha Muhammadu Buhari (@aishambuhari) on


A post shared by H.E Mrs Aisha Muhammadu Buhari (@aishambuhari) on

Muhammad Turad Sha'aban da ne ga tsohon dan majalisar wakilai da ya taba wakiltar mazabar Sabon Gari a Zaria.

Alhaji Mahmud Sha'aban tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna ne a zaben 2007 da na 2011.View this post on Instagram

A post shared by H.E Mrs Aisha Muhammadu Buhari (@aishambuhari) on


Alhaji Sha'aban na rike da sarautar Damburam na masarautar Zazzau. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Turad kwararre ne a harkar kudi kuma mai bada shawara na musamman ne ga tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola.

Hanan ta kammala digirinta a fannin daukar hoto daga jami'ar Ravensbourne da ke Ingila.

SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments