--
Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya


Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, a ranar Alhamis ya ce ya samu bayanin cewa kwamandan Boko Haram gwamna ne a arewa daga bakin wasu 'yan kasuwa da ya hadu da su. A yayin magana a kan tsokacinsa, 

Mailafiya, wanda ya zargi cewa wani gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram ya ce wasu 'yan kasuwa Fulani ne da ya zanta da su a wata kasuwar kauye suka sanar da shi. 

Ya bada hakuri ga dukkan wadanda tsokacinsa ya bata wa rai, ya ce bai yi da niyyar bata wa kowa ba. Ya kara da cewa bai yi niyyar assasa rashin zaman lafiya ba. Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin, wanda ya zanta da wani gidan rediyo, ya zargi gwamnan da yunkurin assasa yakin basasa a Najeriya nan da 2022. 

Gidan rediyon sun gayyacesa ne don yin jawabi a kan harin 'yan bindiga a arewa maso yamma da kuma rikicin kudancin Kaduna da ya tsananta. Bayan wannan zargin, jami'an tsaron farin kaya na jihar Filato a ranar Alhamis sun gayyaci Mailafiya don amsa tambayoyi, inda ya kwashe tsawon sa'o'i bakwai kafin su sake shi. 

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin ya ce ya yi magana ne saboda kishin arewa da kasar baki daya, amma bai san cewa bidiyon zai yadu ba. A wata tattaunawa da Mailafiya yayi da BBC Hausa, Mailafiya ya ce ya amince har yayi hira da mutanen da bai sani ba kuma bai san cewa suna nada ba. "A zatona gidan rediyo ne kadai a Legas," yace. 

Ya ce duk da bai so tsokacinsa ya yadu ba, ba zai iya karyata yin su ba saboda shi masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kuma saboda arewa da Najeriya ne yayi tsokacin. Amma kuma, Kungiyar gwamnonin arewa a ranar Laraba ta yi kira ga cibiyoyin tsaro da su binciki zargin da tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, na cewa "daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya".

A wata takarda da aka fitar a garin Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?