LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta

Rahotanni sun nuna wata yarinya 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo duniya a daidai lokacin da ake yi mata wanka za a kai ta makwanci

Yarinyar ta dawo awanni kadan bayan mutuwa a asibiti, sai dai kuma bayan shafe kimanin awa daya da mutuwa ta sake mutuwa

Lamarin ya faru a kasar Indonesiya ne, inda shugaban rundunar 'yan sandan yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai Wata yarinya 'yar shekara 12 ta dawo duniya a daidai lokacin da danginta ke shirin binneta.

Yarinyar mai suna Siti Mastufah Wardah, an kai ta asibiti a Probolinggo dake Gabashin jihar Java a cikin kasar Indonesia, sakamakon wani ciwo da ya kamata a ranar 18 ga watan Agusta. An bayyana cewa ta mutu da misalin karfe 6 na yamma.

An kai gawarta ga danginta domin su yi mata sallah kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.

Amma a daidai lokacin da ake yi mata wanka, sai kawai gani aka yi idon Siti ya bude cikin ikon Allah sai ta tashi. Mahaifinta mai suna Ngasiyo, mai shekaru 40 ya bayyana halin da ya shiga bayan diyar tashi ta dawo.

"A lokacin da ake yi mata wanka sai yanayin jikinta yayi zafi," ya sanar da manema labarai. "Sai idonta ya bude. Sai muka ji zuciyarta tana bugawa kuma jikinta yana motsi."

An kira likitoci wajen inda suka bawa Siti taimakon gaggawa da zai taimaka mata tayi numfashi da kyau. Sai dai kuma bata jima da dawo ba sai Allah ya kara karbar abarsa. Daga nan aka yi mata wanka aka binne ta a makabarta.

Shugaban rundunar 'yan sanda na Lumbang, Cif AKP Muhammad Dugel ya tabbatar da faruwar lamarin bayan ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru.

"Kwarai da gaske ne wannan lamari ya faru, yarinyar ta mutu ta dawo, bayan an kwantar da ita a asibiti," ya sanar da manema labarai. "A lokacin da ake yi mata wanka ta dawo tana motsi bayan shafe kimanin awa daya, sai ta sake mutuwa."

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments