--
Yanzu yanzu: SERAP ta maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu

Yanzu yanzu: SERAP ta maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu

KungiyarSERAP ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja

SERAP ta shigar da karar ne saboda gazawar Buhari na bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato N800bn daga wajensu

Haka zalika, kungiyar ta bukaci kotun ta tilasta Buhari ya fadi dalilin rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati
Kungiyar kwatowa talaka hakkokinsu da tabbatar da adalci (SERAP) ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

SERAP ta maka shugaban kasar ne saboda gaza bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato N800bn daga wajensu, da kuma ayyukan da aka yi da kudaden.

Shugaban kasar a ranar 12 ga watan Yuni, 2020 ya yi jawabi mai tsayin sakin layi 78, inda ya bayyana cewa gwamnati ta kwato N800bn daga barayin kasa.

Ya sanar da cewa an yi amfani da kudaden da aka kwato wajen gudanar da ayyukan raya kasa a sassa daban daban na kasar.

A takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1064/2020 da aka shigar a ranar Juma'a a kotun, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Shugaba Buhari ya wallafa sunayen mutane da aka kwato kudaden daga wajensu.

Haka zalika ya wallafa ranaku, da wuraren da aka yi ayyukan da har aka batar da kudaden. Haka zalika SERAP na son hukumomin yaki da rashawa su shigo cikin lamarin.

A cikin takardar, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Buhari ya tilasta hukomin yaki da rashawarar su binciki yadda aka rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati a shekarar 2019.

Daga cikin wadanda ake karar akwai Abubakar Malami, Antoni Janar na kasa kuma Ministan shari'a, da Zainab Ahmed, Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa.

Karar da SERAP ta shigar ya biyo bayan 'yancin bayanai (FoI) da ta bukata a ranar 13 ga watan Yuni, 2020 ga Shugaba Buhari, tana mai cewa: "Al'umma na da 'yancin sanin bayanan.

"Yan Nigeria na hakkin sanin yadda aka kashe N800bn da aka kwato daga mahandama da kuma dalilin rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati.

"Yin bayani dalla dalla kan kudaden da ake kashewa na da matukar muhimmanci ma damar ana son a samu fahimta da kara yarda tsakanin gwamnati da al'umar da take mulka."

Lauyoyi Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi, sune suka shigar da wannan kara a madadin SERAP.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu yanzu: SERAP ta maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?