LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanda Mutane 15 suka tsira yayin da gini ya ruso a KanoMusiba ta auku yayin da gini ya ruso a kan wasu mutane mazauna unguwar Kurnar Asabe da ke karamar hukumar Dala ta jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya. Jaridar This Day ta ruwaito cewa, an tafka gagarumar sa'a idan aka samu mutum daya ne kacal ya jikkata yayin da mutum akalla 15 suka tsallake rijiya da baya.


Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar Kano, Mista Sa'idu Muhammad, shi ne ya ba da tabbas kan aukuwar wannan mummunan tsautsayi. Ya ce ibtila'in zubewar ginin ta auku ne da misalin karfe 12.00 na dare a layin Dangawan Jingau da ke unguwar Kurnar Asabe.


 Babban jami'in ya shaidawa manema labarai cewa, wani mutum mai suna Abdurrashid Danjuma, mai shekaru 45, ya samu raunuka yayin da ginin ya rufto a kansa. Muhammadu ya ce a halin yanzu Danjuma yana samun kulawar kwararru na lafiya inda suke bashi magani a gadon wani Asibiti.

Wani karamin jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari ya yayin da ya ke kokarin tashi sama a hanyarsa ta zuwa kasar Australia a ranar Asabar kamar yadda 'yan sanda suka bayyana. Hatsarin jirgin saman ya tona asirin wasu masu safarar miyagun kwayoyi da ke Melbourne kuma an kama mutane biyar da ake zargin suna da alaka da masu safarar kwayoyi a Italiya.

Jirgin kirar Cesna wadda aka cika makil da kilogram 500 na hodar-iblis wato koken ya fado kasa ne yayin da ya ke yunkurin tashi daga wani karamin filin jirgi da ke Papua New Guinea a ranar 26 ga watan Yuli.

'Yan sandan Australia cikin sanarwar da suka fitar sun ce, "Akwai alamun hadama a cikin harkokin kungiyar ta masu safarar miyagun kwayoyin" inda suka ce bisa ga alamu nauyin hodar-iblis din ne ya hana jirgin tashi sama.

An tuhumar mutum biyar din da aka kama a Queensland da Victoria da laifin hadin baki don safarar hodar Iblis kilogram 500 da wasu laifan daban masu alaka da safarar kwayoyin. Za a iya yi wa kowannensu daurin rai da rai idan kotu ta same su da aikata laifin da ake tuhumarsu.

An kama matukin jirgin bayan ya kai kansa wurin yan sanda. Mahukunta sun ce jirgin ya taso ne daga wani karamin gari mai suna Mareeba da ke Papua New Guinea a arewacin Queensland amma ya yi lambo hukuma ba ta gan shi ba. Daga bisani an gano hodar Iblis din da jirgin ya dako a ranar Juma'a bayan bincike a yankin.

An kiyasta kudinsa zai kai Dallar kasar Australia miliyan 80 wanda ya yi daidai da Dallar Amurka miliyan 57. Mutanen da aka kama masu shekaru 31, 36, 31, 33, da 61 duk ana tuhumarsu da laifuka daban daban. Mutum na farko ana tuhumarsa da safarar kwayoyi da almundanar kudi fiye da Dallar Australia Miliyan 1.

Yan sanda sun kuma kwace wasu kadarorinsa da kudinsu ya kai Dallar Australia Miliyan 3.5. Wannan kamun da yan sandan suka yi na yana da cikin kamu mafi girma na muggan kwayoyi a tarihin kasar ta Australia. A shekarar 2016 an taba kama wata hodar-iblis din mai nauyin kilogram 500 a New South Wales.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments