LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Yan sanda na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo, bayan akuyoyin sun lalata musu motar da suke fita aiki da ita

Jami'an 'yan sanda a kasar Ingila na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo - 'Yan sandan dai na neman akuyoyin ne sakamakon lalata musu mota da suka yi da tsakar rana a lokacin da suke kan aiki 

'Yan sandan sun bayar da sanarwar duk wanda yake da masaniya akan wadannan akuyoyi ya taimaka ya sanar da su Jami'an 'yan sanda sun bazama neman duk wani mutumi da yake da labarin inda wasu akuyoyi suke da suka lalata musu motar da suke fita aiki da ita da tsakar rana. 

A cewar wani jami'in dan sanda na kasar ta Birtaniya, 'yan sandan suna neman wadannan akuyoyi da suka bata musu mota, inda suka fita neman shaidu da suke da masaniya akan inda wadannan akuyoyi suke.

A cewar 'yan sandan, an dauki hoton akuyoyin suna tsaye akan saman motar tasu a kusa da Newport a ranar Laraba 19 ga watan Agusta da rana, bayan an kira jami'an 'yan sandan yankin bayan an gano wani bam da aka dasa a wajen tun lokacin yakin duniya na biyu wanda bai tashi ba. 

'Yan sandan sun nemi taimakon sojojin ruwa, wadanda suka taso tun daga Portsmouth domin taya su cire wannan bam. Bayan 'yan sandan sun kammala cire bam din, sun koma motarsu suka tarar da ita akuyoyin sunyi mata kaca-kaca. 

'Yan sandan yanzu suna tambayar ko akwai wanda ya san inda wadannan akuyoyi suke, wanda aka dauki hotonsu.  'Yan sandan sun wallafa wannan rahoto a shafin ofishin 'yan sandan na Facebook, inda suka ce: 

"A wani fili dake yankin Newport an gano wani bam da aka dasa a wajen tun lokacin yakin duniya na biyu wanda bai tashi ba. "

Abokanan aikin mu sun gano wannan bam, kuma sun cire shi. "Sai dai kuma akwai wasu akuyoyi da suka bata mana mota, idan kun gane wadannan masu laifi dake cikin hoton nan ku taimaka ku sanar damu." 


WITNESS APPEAL Hi everyone, Inspector Matt here sharing a quick update I recieved from D shift in relation to an...

Posted by Isle of Wight Police on Wednesday, 19 August 2020


 SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments