LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yahaya Sharif-Aminu: Ba mu da alaƙa da wanda ya yi ɓatanci ga Annabi - Tijjaniyya

Ƙungiyar Tijjaniyya ta nesanta kanta daga Yahaya Sharif Aminu, matashin da Kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa a Kano bayan ta same shi da laifin yin kalaman ɓatanci ga Annabi S.A.W.

Karon farko kenan da ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin addini ta mayar da martani kan hukuncin da aka yanke wa matashin mai shekara 22 ranar Litinin.

Shugaban majalisar zawiyoyin Tijjani a Kano, Malllam Muhammad Nura Arzai ya shaida wa bbc cewa ko kaɗan abin da matashin ya aikata ba sa cikin ladubba da koyarwar Sheikh Ibrahim Inyas.

"Mu almajiran Shehu Inyas muna ganin yanke hukuncin kisa kan wanda ya taɓa martabar Annabi S.W.A ya yi daidai," in ji Muhammad Nura Arzai.

Ku latsa hoton da ke kasa don sauraron cikayyiyar hirar:

 

A ranar Litinin ne kotun da ke zamanta a unguwar Hausawa a birnin Kano ta ce "za a rataye Yahaya Aminu har ya sai ya daina motsi," sai dai ta ce yana da damar daukaka kara.

Tun a watan Maris na 2020 Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge shi da yin ɓatancin a cikinta.

Kazalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Alƙali ya yanke wa Umar Farouq hukuncin ne sakamakon shekarunsa ba su kai 18 kamar yadda kundin manyan laifuka ya tanada.

Ya yi ɓatancin ne yayin da suke yin ce-ku-ce da wani. 

SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments