--
Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya

Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya

Femi Fani Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya rufe wani ɗan jarida, Eyo Charles da zagi saboda ya masa tambaya a yayin taron manema labarai a Calabar jihar Cross Rivers a makon da ga gabata.

Tsohon ministan wadda ya fara ziyarar jihohin da Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ke mulki tun a watan Yuli ya zitarci Cross Rivers a makon da ga gabata. The Cable ta ruwaito cewa a karshen ziyarar, ya kira taron manema labarai inda ya yaba wa ayyukan da Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ya yi.

Baya ga yabon, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tallafawa jihar duba da ƙarancin kuɗi da ta ke da shi. Eyo, wani ɗan jarida mai yi wa Daily Trust aiki ya tambayi tsohon ministan ko wani ne ya dauki ɗawainiyar tafiye-tafiyen da ya yi hakan yasan Fani-Kayode ya fusata ya fara zage-zage.

Fani-Kayode ya kira ɗan jaridar 'wawa' kuma ya ce shi ba talaka bane da zai nemi wani ya biya masa kuɗin tafiye-tafiyen sa.

Ga wani sashi cikin abinda tsohon ministan ya faɗi. "Bari in faɗa a talabijin kowa ya gani. Wane irin tambayar banza ne wannan? Daukan nauyin wa? Ka ko san da wanda ka ke magana? Ba zan amsa tambayar wannan mutumin ba.

"Wace irin tambayar cin mutunci ne wannan? Wace irin ɗaukan nauyi? Wane zai iya bani kuɗi? Da wa kake tunanin ka ke magana? Ka je ka yi ƙaran kan ka zuwa shugaban ka, kada ka zage ni a nan, ba zan amsa tambayar wannan mutumin ba.

"Na gani a fuskarka tun kafin ka iso nan cewa kai wawa ne. Kada ka sake min irin wannan maganar. Ko ka san da wanda ka ke magana? Ƙaramin tunani ka ke da shi, kada ka ɗauka kowa irin ka ne.

"Tun shekarar 1990 na ke siyasa ... An sha daure ni, na wahala. An yi min bita da ƙulli fiye da sauran ƴan siyasar da ka ke bi domin su baka na kashe wa. Kada ka sake min irin wannan, ni ba talaka bane kuma ba zan taba ƴin talauci ba."

Fani-Kayode ya cigaba da kumfar baki da zage-zage inda ya tunatar da ɗan jaridar cewa ya rike muƙamin minista a baya kuma shi lauya ne saboda haka cin fuska ce wani ya yi tsammanin yana bukatar a biya masa kuɗin tafiye-tafiyen sa.

Bayan ya kammala zazzage abinda ke cikinsa, ya tambayi ko sauran ƴan jaridar na da sauran tambaya inda suka ce a'a sannan ya yi tafiyarsa. Babban sakataren watsa labaran gwamna Ayade, Christian Ita ya yi ƙoƙarin bawa Ministan haƙuri amma bai haƙura ba ya cigaba da zagin ɗan jaridar.

A watan Yuli, Masarautar Zamfara ta naɗa Fani-Kayode sarautar "Sadaukin Shinkafa" wadda hakan ya janyo wasu masu sarauta sunyi murabus.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI 

0 Response to "Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?