--
Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa -Aisha Yesufu

Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa -Aisha Yesufu

Jagorar kungiyar rajin ceto yan matan Chibok BBOG, Aisha Yesufu, ta caccaki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan bayyana niyyarsa na rattafa hannu kan hukuncin kisan da akayiwa mawaki, Yahaya Sharif-Aminu. Yahaya Sharif-Aminu dai ya yi maganar batanci ne ga Manzon Allah (SAW).

Aisha Yesufu wacce ta shahara wajen caccakan shugabanni ta yi jawabi a ranar Juma'a cewa shi ma Ganduje a yanke masa hukuncin kisa kan laifin karban rashawa. Tace: "An kama Ganduje dumu-dumu kan Kamara yana karban cin hanci.

A dokar Shari'a, duk kyautan da aka baiwa ma'aikacin gwamnati na gwamnati ne, ballantana karban cin hanci." "Babu garkuwa a Shari'ar Musulunci. Ganduje ya kamata a yankewa hukuncin, ba shi ya rattafa hannu kan hukuncin kisa ba."

A ranar Alhamis, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis ya ce a shirye ya ke ya saka hannu domin a zartar da hukuncin kisar da kotu ta yanke wa mawaƙi Yahaya Sharif-Aminu da ya yi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).

Idan za a iya tunawa babban kotun Shari'a da ke Kano ta samu Aminu-Shariff da laifin batanci kuma ya yanke masa hukumcin kisa ta hanyar rataya. A watan Maris ɗin shekarar 2020, mawaƙin mai shekaru 22 ya rera wata waƙa mai ɗauke da batanci ga Manzon Allah ya tura a dandalin sada zumunta ta WhatsApp,

hakan ya sa mutane suka harzuƙa. Da ya ke jawabi bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, Ganduje ya ce kotu ta bawa wanda aka yanke wa hukuncin wa'adin kwanaki 30 don ɗaukaka ƙara, idan bai ɗaukaka karar ba shi kuma ba zai bata lokaci wurin rattaba hannu a kan hukuncin ba.

Source: Legit

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa -Aisha Yesufu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?